Cika shekara daya: Minista Sadiya ta yabi ‘yan jarida da ma’aikatan agaji

0

Ministar Harkokin Agaji Da Jinƙai, Hajiya Sadiya Umar Faroukh, ta yaba da kokarin kafafen yaɗa labarai, ma’aikatan agaji da hukumomin hadin gwiwa a daidai lokacin da ma’aikatar ta ta cika shekara daya da kafawa.

Ita dai wannan ma’aikata, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya kirkire ta a ranar 21 ga Agusta, 2019 domin aiwatar da manufofi da ayyukan agaji, da rigakafin aukuwar bala’o’i tare da kai agajin gaggawa, sa’annan da gudanar da aikace-aikacen taimaka wa jama’a mabukata.

A cikin wata takardar sanarwa da mai agaza mata a harkar aikin yada labarai Halima Oyelade ta raba, ministar ta yi la’akari da cewa “wannan shekara ce da aka yi abubuwa da dama, mai cike da kalubale da abubuwan sha’awa wadda a cikin ta mu ka koyi hanyoyin kai agaji ga jama’a da kula da bala’o’i, amma a duk cikin ayyukan mun maida hankalin mu wajen cika aikin da aka ba mu wanda ya ƙunshi kai wa jama’a dauki, hana aukuwar bala’i tare da agaza wa wadanda bala’i ya auka mawa, da kuma fito da hanyoyin rage raɗaɗin bala’i idan ya faru, wanda hakan ya taimaka mana wajen inganta aikin mu saboda nan gaba.”

A lokacin da ta ke yaba wa Shugaban Kasa a kan hangen nesa da ya yi na kirkiro ma’aikatar wadda ta kasance kan gaba wajen yaki da annobar korona, Hajiya Sadiya Umar Farouq ta gode masa saboda dora ta a kujerar direbar ma’aikatar da ya yi.

Haka kuma ta yi la’akari da cewa a cikin wannan shekara dayan, ta koyi muhimman darussa tare da samun sabuwar fahimta game da hanyoyi masu bullewa da marasa bullewa a wannan aiki.

Yayin da ta ke yaba wa kafofin yada labarai, ministar ta ce wadannan kafofi abokan tafiya ne wadanda tilas ne a hada karfi da su don samun nasara.

Ta ce, “Ina so in bayyana maku a yau cewa aikin da ku ke yi ya dace.”

Ta ce da yake ba hurumin ta ne ta bai wa kan ta maki kan nasarorin da ta samu ba, amma a shirye ta ke ita da abokan aikin ta za su ci gaba da aikin su a cikin sadaukarwa da jajircewa don cika alkawurran aikin su, wanda ya yi daidai da jigon cikar su shekara daya – wato Service2Humanity.”

Ministar ta yi jinjina na musamman ga “ma’aikatan agaji da kuma abokan hadin gwiwar mu a wannan sashe daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya irin su OCHA, IOM, UNHCR da Hukumar Abinci ta Duniya, Bankin Duniya, USAID da Tarayyar Turai (EU), da kuma sauran hukumomin haɗin gwiwa wadanda su ka ci gaba da bada agaji duk da halin rashin tsaro da ake ciki da kuma wahalhalun da su ke fuskanta.

Ta kuma yi jaje kan wadanda su ka rasu a wuraren da ake da rashin tsaro a cikin wannan shekara dayar da ta gabata.

Ministar ta yi bayanin cewa cika shekara daya da kirkiro ma’aikatar ya sa tilas su dage sosai.

Ta ce, “A yayin da mu ke murnar cika shekara daya, ina so in ce lokaci ya yi da ya dace mu sake zage dantse wajen aiwatar da aikin mu. Dole ne mu nemo hanyoyin da za mu fadada aikin kula da bala’o’i, samar da agaji da kuma fito da hanyoyin tallafin jama’a wanda hakan zai taimaka mana wajen inganta aikin mu a nan gaba.”

Share.

game da Author