Cigaban matasa a gobe ya ta’allaka ne ga aikinsu na yau, Daga Nura Mafita

0

A mahangata matasa zasu sami cigaba ne kadai bayan rungumar tsarin tafiya tare domin tsira tare.

Kowace al’uma tana iya samun cigaba ne madamar an inganta rayuwar matasa, wace hanya matasa ke kokarin kawo canji?

Ga misali shugaba Muhammadu Buhari ya canza jam’iya daga App zuwa ANPP daga ANPP zuwa CPC daga CPC zuwa APC

Amma kasancewar masu rike da shugabancin jam’iyu ba matasa bane sune ummul’aba’isin ba’a samun tikitin takarar a kowace jam’iyar, matasa nada rawar da zasu taka wajen kawo cigaba

Ya zama wani wagambari ace shugaban jam’iya matashi ne a mazaba, gunduma, jaha ko kuma Tarayya, ta wace hanya kuma za’a iya zabo matashi domin hayewa a zaben raba gardama ?

Ni a mahangata matasa baza su iya samun adadin da ya dace ba na rabon muqamai madamar ya zamana basu ne da alhakin zabar shugabanni daga fari ba wato zaben fidda gwani

Ni a mahangata kasancewar cigaban ilimi da ruwan sha, da sauran ababen more rayuwa ya ta’allaka ne ga matasa amma sai sun canza sun sami damar kafa shugabanci daga jam’iya zuwa mulkin mai kasafin kudi.

Duk mutanen da matasa ke zabowa a zaben secondary election wato zaben raba gardama karasa aiki ne na tsofaffin, wato kamar dattawa, da manyan jam’iyya Wanda ako wace jam’iya haka tsarin yake, su ke kawo Dantakara, kaga ko linzaminsu ahannun tsofaffi yake.

Ko shugaba Buhari da matasa ke kurin sun kawo canji ba aikinsu bane, aikin ‘yan mazan jiya ne, tun daga bangaren PDP, Wadanda suka yi maja da APC zuwa masu zaben fidda Gwani.

A fahimtata lokaci ne da matasa zasu fara fadada tunaninsu wajen aiki tuquru tare da sakankancewa cewar cigaba zai samu ne kadai ga aiyukanmu na yau da shirin da muka yi a yau.

Babu wata Kasa da take iya samun cigaba sai ya zama matasa na cikin kunshin shugabanci.

Koda a aikin Gwamnatin, Aiki ga kamfanoni matasa sun zama na gaba – gaba wajen kawo cigaba da bunkasa.

Manufar muqalar dai a kowane sashe matasa nada wakilci domin da su ne kadai ake iya bunqasawa da dabbaqawa a kowane tsari.

Matasa na iya kawo canji da samar da ingantanccen shugabanci domin dorawa daidai da bukatar zamanin da muke ciki.

Matasa da sauran Gyara

Daga Nura Mafita
Mazaunin Sharada

Share.

game da Author