CHAMPIONS LEAGUE: Magoya bayan PSG sun barke da kone-kone saboda takaicin Bayern Munich ta yi nasarar lashe kofi

0

Yayin da ‘yan wasa da magoya bayan Kungiyar Bayern Munich suka barke da murna da shagulgulan lashe Kofin Zakarun Turai na Champions League, a birnin Paris kuma mummunar zanga-zanga ce ta barke, inda magoya bayan PSG suka fita kan titina, musamman a dandalin da suka yi niyyar yin shagalin lashe kofi, suka rika banka wa dukiyoyi da motoci wuta, saboda takaicin rashin nasara.

Bayern Munich ta yi nasara a kan PSG, inda ta lashe kofi karo na 6. Kusan a duniya kowa ya sa ran cewa Bayern za ta yi nasarar lashe kofi, saboda irin dukan binne kulob a makabarta da ta rika yi wa duk wata kungiyar da ta tarbi gaban ta, tun farkon fara gasar, har zuwa ranar Lahadi lahadi da ta yi nasara a kan PSG, wadda ita ma ta yi ta kokarin ganin ta lashe kofin a karo na farkon tarihin kafa kungiyar.

Dalilan Kone-kone A Birnin Paris:

1. Ko shakka babu PSG ta kai kan ta har wasan karshe a cikin gagarimin shirin cin kofi, idan aka yi la’akari da irin kungiyoyin da ta fatattaka kafin kaiwa ga wasan karshe.

2. PSG ta yi kuskuren irin gagarimar murnar da suka rika yi saboda sun kai ga wasan karshe, bayan sun yi nasara a kan Liezpieg ta Jamus. Sun rika kallon cewa da sun shiga fili a wasan karshe, tamkar hannu kadai za su mika a damka musu kofi.

3. Idon su ya rufe daga tunanin cewa da FC Bayern Munich za su kafsa wasan karshe, kungiyar da ta zubar wa Barcelona hakora 8 a naushi daya da ta yi wa kungiyar a wasan kusa da na kusa da karshe.

4. Ganin da PSG ta yi cewa kwallo daya tak aka ci su, ba kamar irin su Barcelona da aka zabga wa 8 ba, ya bata wa magoya bayan rai, har suka shiga kone-kone a birnin Paris a cikin dare.

Darasi 10 Bayan Nasarar Bayern Munich A Gasar Champions League:

1. A tarihin Champions League, Bayern Munich ce kungiyar da ta fara kafa tarihi a bana, inda tun daga wasan farko a ‘gurup’ har wasan karshe, babu wasan da ba ta taba jefa kwallo a ragar kungiyar da ta kafsa da ita ba.

2. Bayern Munich ta kafa tarihi a karon farko a Champions League, tun daga wasan ‘gurup’ ba ta taba yin kunne-doki a gasar ta bana ba. Sai dai nasara a kan kowane kungiyar da suka hadu.

3. Dan wasan Bayern Munich Coman, wanda ya jefa kwallo ragar PSG, daga kulob din aka gaji da shi, aka bada aron sa a Bayern, saboda an gaji da dumama bencin da ya ke yi a kulob din. Ashe shi ne zai dumama wa PSG takaicin da ya yi sanadiyyar magoya bayan ta babbake birnin Paris, saboda haushi da takaici.

Babban abin takaicin kuma shi Kingsley Coman, dan kasar Faransa ne, amma ya kwana murna a Jamus, ya sa Faransawa kwanan bakin ciki.

Kingsley Coman yanzu haka shekarun sa 24, amma ya ci kofi daban-daban har 24

4. Robert Lewandowski ne ya fi cin kwallaye har 15 a wannan gasar Champions League ta 2019/2020.

5. Serge Gnabry wanda ya taimaka wa Bayern zuwa wasan karshe, daga Arsenal aka yi masa kora-da-hali, aka bada aron sa ga West Bromwich Albion a 2015. Daga can Arsenal ta sayar da shi arha tibis ga Bayern.

6. Gaba dayan farashin jimlar fam €90 milyan Bayern Munich ta sayo ‘yan wasa 11 da suka fara taka kwallo da Barcelona da kuma PSG. Amma Harry Maguire €80 milyan cur Manchester ta zuba kudi ta sayo shi. Har ya ma fi adadin kudaden da Real Madrid ta sayo Modric, Casemiro da Tony Kroos su uku.

7. Bayern Munich ta janyo wa Barcelona asarar €5 milyan sanadiyyar lashe Kofin Zakarun Turai da ta yi. Akwai yarjejeniyar cewa idan Coutinho ya lashe kofi a Bayern, to Barcelona za ta biya Liverpool €5 milyan.

8. Bayern Munich ta kafa tarihin da ta jefa kwallaye 42 a wasanni 11 kacal a kakar gasar Champions League ta 2019/2020. Barcelona ce ta taba cefa kwallaye 44, amma a wasanni 16, a gasar 1999/2000, ba wasanni 11 ba kamar Bayern.

9. Tun daga shekarar 2000 har 2020 duk kulob din da ya je wasan karshe a Champions League bai yi nasara ba: Valencia a 2000, Leverkusen a 2002, FC Monaco a 2004, Arsenal a 2006, Chelsea a 2008, Liverpool a 2029, sai kuma PSG yanzu a 2020, duk kashi suka kwasa, ba su dauki kofi ba.

10. PSG ta yi canjaras da Real Madrid wajen kafa tarihin jefa kwallaye a wasannin Champions League masu yawa a jere.

Daga 2016 zuwa 2020, PSG ta jefa kwallo a wasanni 34. Kamar yadda ita ma Real Madrid ta jefa kwallo a wasanni 34 daga 2011 zuwa 2014.

Share.

game da Author