CACAN BAKI: Rundunar Soji ta karyata korafin Gwamna Zulum, ” Boko Haram suka far maka ba Sojoji ba”

0

Rundunar Sojin Najeriya ta karyata korafin gwamnan Barno, Babagana Zulum ikirarin da yayi cewa sojoji ne suka bude masa wuta ba Boko Haram a garin Baga dake karamar hukumar Kukawa.

Kodinatan yada labarai na rundunar Sojin, John Enenche ya karyata wannan zargi na gwamna Zulum yana mai cewa binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa Boko Haram ne suka bude wa tawagar gwamnan wuta a Baga ba sojoji.

” Abin da ya faru shine bayan wannan zargi da gwamna Zulum yayi akan dakarun mu, sai muka kaddamar da bincike mai zurfi akai. Da farko dai yadda aka yi wannan harbi ba yadda sojojin mu ke harbi bane. Akwai rashi kwarewa a ciki.

” Akwai yadda sojojin mu ke harbi yadda aka koya musu a wajen daga. Sannan kuma mu da muka san yadda Boko Haram ke kai hare-haren su mun tabbatar ba sojojin mu bane, haka kuma bincike ya nuna lallai ba su bane Boko Haram ne.

Idan ba a manta ba gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya bayan artabu da masu tsaran sa suka yi da Boko Haram a hanyar Baga zuwa zuwa Maiduguri.

Sai dai kuma bayan fatattakar su da jami’ai suka yi, daga baya gwamna Zulum ya shaida wa wakilin Talbijin din Channels cewa ba Boko Haram bane suka far masa a Baga.

” Da gangar sojoji suka bude min wuta saboda wata manufa ta su da ban sani ba. Amma tabbas ba Boko Haram bane.

Ya ce sojoji na yi masa bita da kulle a aikin ganin zaman lafiya ya dawo garin Maiduguri da yake yi babu kakkautawa.

Share.

game da Author