Shugaba Muhammdu Buhari ya nuna takaicin yadda rigingimun rashin dalili su ka dabaibaye jam’iyyar APC.
A ranar Litinin Buhari ya ce maganin abin shi ne a rika tuntubar juna da bangarori domin a lalubo maslaha.
Cewa ya yi a haka ne za a kara inganta tasirin jam’iyyar da kuma yiwuwar sake lashe zabe.
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin da ya kunshi bangaren Gudanarwa, Majalisa da kuma shugabannin jam’iyya, a Fadar Shugaban, domin tuntuba da kuma warware rikirkitattun batutuwa da rigingimun da suka dabaibaye APC.
” Bari na yi muku marhaban lale da zuwa irin wannan taron kwamiti na farko na APC.
“Jam’iyyar mu ke da rinjaye a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya. Mataimakin Shugaban Kasa, Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Tarayya duk ‘yan APC ne. Kuma aiki tsakanin mu da Majalisa na tafiya daidai.
“Amma duk da haka jam’iyyar sai ruftawa cikin rintsi rikice-rikice ta ke yi, wadanda wasu ma ba su day wani dalili. Wadannan rikice-rikice na haifar mana da asarar kujerun Majalisar Dattawa da na Tarayya, har da rashin kujerun gwamnoni. A gaskiya bai kamata mu tsinci kan mu a wannan baudadden yanayi ba. Tilas mu magance haka ta hanyar kafa wannan kwamiti na tuntuba.
Daga nan sai ya yi kira da a kara zage damtse kuma a yi aiki bisa cika alkawurran da aka daukar wa talakawa.
“Na yi imani da tsarin kowace bangaren gwamnati ya yi zaman kan sa, ba tare da ana yi masa shisshigi ba..”
Mambobin kwamiti sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yeni Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakin sa, Shugaban Majalisar Tarayya da Mataimakin sa, Shugaban Jam’iyyar APC, Mala Buni, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Masu Rinjayen Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi, Shugaban Masu Rinjayen Majalisar Tarayya, Ado Doguwa.
Sauran sun hada da Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.