Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kori Kodinetan shirin yin afuwa ga tsegurun yankin Neja Delta, Charles Dokubo.
Sai dai kuma sanarwar wanda kakakin fadar shugaban Kasa ya saka wa hannu bata fadi dalilin sallamar Dokubo ba.
” Shugaban Buhari ya nada Col. Milland Dixion Dikio mai Ritaya sabon shugaban shirin na rikon kwarya. Sannan kuma an umarci Dokubo ya mika duka kayan aiki ga babban darekta a wannan ofis.
A karshe shugaba Buhari ya godewa dokubo sannan yayi masa fatan alkhairi.
Idan ba a manta ba, tsohon shugaban Kasa Marigayi Umaru Yar’adua ne ya kirkiro da wannan shiri domin tallafawa tsagerun matasan yankin Neja Delta.