Buhari ya amince a kafa cibiyar dakile bazuwar makamai

0

Shugaba Muhammdu Buhari ya amince a kafa Cibiyar Dakile Bazuwar Manya da Kananan Makamai. Mashawarci a Bangaren Tsaro, Babagana Monguno ne ya bayyana haka.

Wannan sabuwar cibiya idan an kafa ta, za ta kasance a karkashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro. Haka dai Monguno din ya shaida wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa.

Ya kara da cewa cibiyar za ta kasance irin Cibiyar Dakile Ta’adanci, wadda ita din ma a karkashin kulawar sa ta ke.

Akwai tsoffin shugabannin Najeriya a wurin taron da Buhari ya amince da kafa wannan cibiya.

Ya ce idan aka cibiyar, za ta yi aiki ne a bisa ka’idojin da kasahen duniya da kuma ECOWAS suka gindiya dangane da batun haka bazuwar makamai.

Ya kuma kara yin bayani cewa cibiyar za ta hana safarar makamai tare da tattara dimbin makaman da aka kama ana kalata su.

“Shugaba Buhari ya amince da kafa cibiyar ce bisa shawara ta. Kuma za ta kasance a karkashin kulawar ofishi na, na Mashawarci a Bangaren Tsaro.” Cewar Moguno.

Monguno ya ce Buhari ya nemi a kara salon tsimakekeniyar juna da bayanan tsaro, a tsakanin Sojojin Najeriya da sauran bangarorin tsaron kasar nan.

“Ana tsare-tsaren amfani da jirage masu tuka kan su, wato ‘drones’ wajen yin sintiri a fadin kasar nan domin dakile masu garkuwa da mutane.

Rahoton wata kungiya ya nuna an kashe mutum 415 a kashe-kashen gilla a Najeriya.

Share.

game da Author