Tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo, ya maida martani dangane da irin kakkausar wasikar ta’aziyyar da ya rubuta kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu, dan asalin Jihar Ogun.
Obasanjo a cikin wasikar ta’aziyya, ya ce Kashamu ya tsere wa hukuncin Kotun Amurka da ke tuhumar sa da laifin hada-hadar kwaya, amma gudun da ya yi, bai iya tsere wa mutuwa ba.
“A rayuwar Sanata Esho ya yi duk wata dabarar kauce wa hukuncin Kotun Amurka da ke tuhumar sa da hada-hadar muggan kwayoyi.
“Amma babu wani tsimi ko dabarar da ta iya hana mutuwa zuwa gadan-gadan ta dauki ran sa. Saboda shi ajali idan ya zo, to babu makawa tafiyar da babu dawowa ce ta zo.
“Allah ya gafarta masa, ya yafe kura-kuran sa, ya kai shi gidan Aljanna.” Inji Obasanjo.
Sai dai kuma wannan wasika ta Obasanjo ta harzuka mutane da yawa, inda suka rika nuna cewa Obasanjo bai yi dattako ba. Sun nuna cewa murnar mutuwa dai murnar wofi ce kawai, tunda kowa ma mutuwa zai yi.
Cikin wadanda suka maida wa Obasanjo martani, har da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose.
Fayose ya ce ba tarbiyyar kwarai ba ce a ce mutum ya mutu, sannan kuma a rika aibata shi.
“Ni a cikin al’ummar da na tashi, idan mutum ya mutu ba a aibata shi, komai laifin da ya yi.”
Fayose ya ce zai gani idan da rai da nisan kwana irin tunawar da jama’a za su yi wa Obasanjo bayan mutuwar sa.
Mutane da yawa na da wannan ra’ayi irin na Fayose, sai dai kuma Obasanjo ya ce bai damu ba, duk abin da mutum zai fadi bayan babu ran sa a duniya.
“Ni mene ne ruwa na. Idan na mutu duk abin da mutum zai fada kai na, ya je ya fadi, shi ta shafa.
“Shin yanzu da na ke da rai, wane irin zagi ne mutane ba su yi min? Yo ni duk abin da mutum zai fadi idan na mutu, ya je ya fada mana. Wannan ai matsalar sa ce.
“Ko ka aibata ni, ko ka yabe ni, ban damu ba. Yadda mahalicci na ke gani na shi ne abu mafi cikakken abinda zai dame ni ko ya faranta min.” Cewar Obasanjo.