Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya bayyana cewa jihohi 16 sun karbi kudin da Bankin Duniya ya rabawa jihohin Najeriya domin rage radadin Korona.
Gwamna Sule yayi wannan bayani bayan taron Kasa da aka yi ta yanar gizo wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
” Bankin ya baiwa kowacce jiha naira miliyan 100 domin rage radadin Korona a jihohin su.
” Jihohin sun hada da Ekiti, Gombe, Niger, Sokoto, Taraba, Oyo, Abia, Enugu, Zamfara, Bauchi, Ebonyi, Kaduna, Kwara, Cross River, Imo da Delta.
Sule ya kara da cewa sauran jihohin da basu kammala cika fom din su ba domin samun wannan kudi. Sai dai ya ce akwai wasu jihohin biyar da za a basu nan ba da dadewa ba.
Jihohin su ne, Plateau, Yobe, Ondo, Benue da Osun
Gwamna Sule ya baya ga haka, an tattauna batun tsaro a wannan taro da kuma yadda za a wadata jihohi da kudade domin tunkarar wannan matsala da ya ke neman ya fi karfin su daga gwamnatin tarayya.
Bayan haka shugabannin rundunonin tsaron Najeriya sun yi bayanai kan ayyukan da suke yi na samar da tsaro a kasar nan da kuma halin da ake ciki a yanzu.
Gwamna Sule ya ce za a ci gaba da tattauna wasu matsalolin da ake fama da su a kasa nemo hanyoyin da za a bi don shawo suko da a bayan wannan taro.