‘Ban taba zuwa wurin shugaba Buhari don in nemi ya canja wani hafsan tsaron kasa ba – Zulum

0

Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya bayyana cewa dole gwamnati ta maida hankali wajen tsananta maida ‘Yan gudun Hijira garuruwan su domin su ci gaba da noma da kiwo da sauran sana’o’in da suke yi idan ba haka ba kuwa za su ci gaba da fadawa kungiyar Boko Haram.

Zulum ya ci gaba da cewa gwamnati ta gaza wajen wadata ‘yan gudun hijira da abincin da za su ci ya ishe su a sansanonin su.

Zulum ya bayyana haka da kuma wasu shawarwari da gwamnatin sa ta dauka a tattaunawa da yayi da BBC Hausa.

Sannan kima ya ce bai taba zuwa wanen shugaban Kasa don ya nemi a canja ko a cire wani shugaban rundunar tsaro ba. Ya ce ya dai nemi a gyara matsalolin da sonoji da sauransu ke fama da su.

A cewar sa a lokacin tattaunawarsa da BBC Hausa din Zulum ya ce ” A Gaskiya ne kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne,” in ji gwamnan.

“idan har jama’ar da ke sansanonin ‘yan gudun hijra a jihar Borno ba su samu abin da suke so ba musamman damar komawa garuruwansu domin noma to fa dole ne su shiga kungiyar Boko Haram.

“Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra. Ba sa samun abin da suke so. Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar da ciyarwa gare su mai dorewa,” a cewar Gwamna Zulum.

Daga nan sa ya kara da cewa gwamnatin sa ta yi nasarar maida wasu da dama garuruwan du musamman yan kananan hukumomin Kukawa da Mafa, kuma har yanzu gwamnati na shirin maida na Kawuri garin su.

“Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala”.

Dubban mutane ne suka rayukan su da muhalli a dalilin hare-haren Boko Haram a jihar Barno.

Share.

game da Author