Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana wa BBC Hausa cewa kamata yayi mulki ya koma yankin kudancin Najeriya ne bayan Shugaba Buhari ya kammala zangon sa ta biyu.
A doguwar hira da yayi da BBC Hausa, gwamnan jihar ya ce bashi da ra’ayin takarar shugabancin Najeriya yanzu kamar yadda ake da watsawa tun yana ministan babban birnin tarayya.
Ga kalaman gwamna El-Rufai kamar yadda ya zayyana wa BBC Hausa.
“Ana cewa ina son shugabancin kasa tun ina ministan Abuja, wannan shirme ne. Allah shi yake ba da mulki, ko kana so ko ba ka so idan yana so zai ba ka amma ni ban taba neman shugabancin Najeriya, ba wanda zai ce na taba nema,”
“A siyasar da ake yi a Najeriya, akwai tsarin da ake bi na karba-karba, inda kowa ya amince cewa idan arewa ta yi mulki shekara takwas, kudu za ta yi mulki shekara takwas.”
Ya ce duk da ba a rubuta tsarin karɓa-karɓan a tsarin mulki ba, amma kowane ɗan siyasa a ƙasar ya san da shi.
“Shi ya sa na fito na ce bayan Shugaba Buhari ya yi shekara takwas, ka da wani ɗan arewa ya nemi muƙamin. A bar ƴan kudu suma su sami shekara takwas.”
Ya ce shi karan kansa cancanta yake bi wurin bai wa mutum aiki.
“Idan ka kalli yadda nake, ba na ɗaukar mutum ya yi aiki tare da ni domin shiyyar da ya fito. Cancanta na ke dubawa, ina duba wanda idan aka ba shi amanar jama’a zai riƙe ta yadda ya kamata,” a cewar gwamnan.