Babu wani tubabben Boko Haram da aka dauka aikin soja – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta karyata ji-ta-ji-tar cewa an kwashi wasu tubabbun ‘yan Boko Haram an shigar da su cikin sojojin Najeriya.

Wannan ji-ta-ji-ta dai ta rika yawo a soshiyal midiya, kamar wutar-daji, har dimbin jama’a suka rika yin tir da shirin kankare akidar ta’addanci da gwamnatin Shugaba Muhammdu Buhari ke yi wa tubabbun ‘yan Boko Haram.

Ji-ta-ji-ta ta kara tsanani, bayan da Gwamnan Jihar Yobe, Babagana Zulum ya ce sojoji ne suka kai wa tawagar sa hari, ba Boko Haram ba.

Da yawan jama’a sun rika cewa tubabbun ‘yan Boko Haram ne da suka shiga aikin soja, suka kai wa Zulum hari.

Sai dai kuma cikin wata sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta fitar, wadda Garba Shehu ya sa wa hannu, ya ce hakan ba gaskiya ba ne.

“Ya na da kyau jama’a su sani cewa babu wani tubabben dan Boko Haram da aka dauka aikin soja, kuma babu wani shiri mai kama da haka da ake kan yi a yanzu ko nan gaba.” Inji shi.

Daga nan ya bayyana muhimmanci da halascin shirin cewa Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Dakile Gudun Hijira ta Duniya ce suka karfafa a rika yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram, don kada su sake tuburewa.

“Shi wannan shirin tubabbun bai hada da gaggan ‘yan ta’adda, wadanda sun-ci-dubu-sai-ceto ba. Ya danganci burbushin wadanda sojoji suka damke ne, aka tilasta su ajiye makamai.”

Ya ce manyan kungiyoi na duniya sun bada shawarar yin haka, bayan nazarin da suka yi a wasu kasashe masu kamanceceniya da irin matsalar ‘yan ta’addar Najeriya, inda a can aka rika gudanar da irin wannan shiri kuma aka samu nasara.

Shehu ya ce kamata ya yi al’umma su daure su sake karbar su, saboda sun tuba. Domin idan suka rasa yadda za su yi, kada kuma su sake daukar makamai su koma aikata ta’addanci.

Share.

game da Author