Ba za mu bari a yi rufa-rufa da kashe-kashen Kudancin Kaduna ba – Osinbajo

0

Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ba za ta bari a yi rufa-rufa da kashe-kashen kudancin Kaduna. ” Gwamnati za ta bi diddigin wannan kashe-kashe da yaki ci yaki cinyewa.

Bayan haka Osinbajo ya kalubalance mahukunta a jihar da su maida hankali matuka wajen tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu yana da hannu wajen tada zaune tsaye a wannan yanki.

” Dole a bi diddigi a tsamo wadanda ke tafka ta’addanci a wannan yanki kuma a hukunta su, idan ba haka kuwa za aci gaba da samun rashin zaman lafiya a yankin ta yadda wasu za su rika yin abinda suka ga dama da gadara da yin haka.

” Kashe-Kashen da ake yi a kudancin Kaduna ya yi tsananin gaske kuma abin tashin hankali ne. Muna mika ta’aziyyar mu ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su. Amma gaskiyar magana shine rikicin abu ne da za a iya hana faruwar sa tun farko.

Osinbajo ya kara da cewa shi da kansa ya gana da shugabannin addini na yankin kuma ya tattauna da gwamnan jihar domin ganai an kawo karshen kashe kashen Kaduna.

Sannan kuma ya yabawa taron zaman lafiya da kungiyoyin Kataf da na Fulani da suka yi domin sasanta tsakanin su. Wannan zama da sukayi yayi kyau matuka domin zai samar da daidaituwa a tsakanin hasalallun kungiyoyin.

Wadannan na daga cikin jawabin da Osinbajo yayi a taron kungiyar Lauyoyi na Kasa wanda da karfin tsiya a soke gayyatar El-Rufai bayan kungiyar ta gayyace shi.

Share.

game da Author