Fadar Shugaban Kasa ta karyata zargin cewa jami’an SSS sun gayyaci tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na’Abba, saboda magannanun da ya yi kwanan nan a kan Shugaba Muhammdu Buhari.
Cikin wata sanarwa da Garba Shehu, Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa ya fitar ranar Lahadi da yamma, ya bayyana Na’Abba wani mutum ne mai neman suna kawai a ywnzu, wanda ba ya bukatar Fadar Shugaban Kasa ta tsaya bata lokacin maida masa martani.
PREMIUM TIMES ta buga labarin kiran da Na’Abba ya yi wa ‘yan Najeriya su yi tururuwar shiga kungiyar NCFront, mai rajin neman “ceto Najeriya daga baudaddiyar hanyar da mulkin Buhari ya dora Najeriya a kai, har ta ke neman ruftawa wawakeken ramin da babu mai iya tsamo ta.”
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya su hada karfi wajen kirkiro sabuwar mikakkiyar turbar da za a dora Najeriya.
Na’Abba ya yi wannan kalami ne a wurin taron manema labarai na duniya da NCFront ta shirya a ranar Litinin
Ya kara da cewa irin yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya a yanzu, akwai kwakyariya, gargajiganci da harankazama.
Sai dai kuma Fadar Shugaban Kasa ta maida masa raddin cewa ya kamata jama’a su yi watsi da batun surutan da Ghali ke yi ko ya rigaya ya yi, tare da cewa a yanzu ta sa ta kare, ya zama mutumin da ya gama sagarabtun sa da banke-banken hauragiya.
“Mun gano cewa gayyatar da SSS ta yi wa Ghali ba ta da nasaba da shirmen surutan harankazamar da ya rika furtawa, wanda sam bai ma jawo hankalin fadar shugaban kasa ba. Haka duk wani dan siyasar da ya san abin da ya ke yi, bai maida hankali a kan giribtun da Ghali ya rika yi ba.”
Akwai ‘yan siyasar da suka san abin da suke yi, wadanda idan suka yi magana Fadar Shugaban Kasa kan maida musu martani, saboda su ko tari yi, zai ja hankulan jama’a.”
Daga nan Shehu ya shawarci Ghali ya daina gaganiyar tsoma Buhari cikin duk wani mawuyacin halin da ya samu kan sa a ciki.