Ba a saka ko sisi a asusun faston da ke da kusancin kut-da-kut da Magu – Bankin FCMB

0

Hukumar Gudanarwar Bankin FCMB has karyata ji-ta-ji-ta cewa an kimshe naira milyan 573 cikin asusun ajiyar wani fasto a FCMB. Faston an ce makusancin tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ne, kuma Magu din ake zargin ya tura masa kudaden.

An dakatar da Magu sanadiyyar zargin wawurar makudan kudaden da EFCC ke kwatowa da aka yi masa.

Zargin wanda ya fito daga bakin Ministan Tsaro Abubakar Malami, wanda hakan ya sa aka dakatar da Magu ake bincike.

Magu ya shaida wa Kwamitin Ayo Salami mai binciken sa cewa Malami makaryaci ne kuma mashararrancin da ya rika yi wa EFCC kafar-ungulu.

Ranar Litinin da ta gabata ne wasu jaridu suka buga labarin cewa Shugaban Bankin FCMB, Adam Nuru ya shaida wa Kwamitin Salami cewa ys zuba naira milyan 573 a asusun wani fasto a madadin Magu, amma a bisa kuskure. Sunan faston Godwin Omale.

Omale wanda wani babban fasto ne, ya bayyana Magu a matsayin dan sa da ya ke yi wa addu’o’in neman tsari da kuma yin nasara kan ayyukan da ya sa gaba.

Cikin sanarwar da FCMB ta fitar a ranar Labara, wadda Shugaban Hulda da Jama’a na bankin mai suna Diran Olojo ya sa wa hannu, ya ce ba su taba saka wadansu kudade makamantan haka ko kuma haka din a asusun fasto din ba.

Ya ce abin da ya faru matsala ce ta na’urar kwamfuta, kuma hakan ya nuna a Bangaren Hukumar Sa-ido Da Bin Diddigin Hada-hadar kudade (Financial Intelligence Unit). Kudin inji shi ba su shiga asusun fasto din ba, kuskure ne da batan hanya kwamfuta ta yi.

“Shugaban FCMB ya je gaban kwamitin bincike kuma yi masu bayanin cewa rahoton da aka bayar ba gaskiya ba ne, FCMB bai zuba naira milyan 573 a asusun faston da ke da kusanci da Magu ba.

Share.

game da Author