Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed ya yi kirarin cewa tabbas yanzu ‘yan Najerya sun ji a jikin su. idan Allah ya kai mu 2023, jam’iyyar PDP yan Najeriya za su yi.
Gwamna Bala ya fadi haka a tattaunawa da yayi da BBC Hausa, wanda ta wallafa a shafinta.
” Jam’iyyar APC gungun mayaudara ne suka hadu wuri daya da basu yarda da kan su ba ma domin wata manufa. Kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya hada. Da zaran ya kammala wa’adin mulkin sa a 2023 duk za su watse.
” Baka ga tun yanzu ma sun fara samun rarrabuwar kai ba.
” Mu ko a PDP, da ma can mun kware mun goge kuma mun san kan mulki. Tabbas mun yi kuskure amma kuma kuskuren bai taka kara ya karya aka rika yin farfaganda akai, kuma farfagandar karya ma yau gashi ana ganin abin da ya faru a hukumar NDDC, ga kuma EFCC.
” Da ance mune Boko Haram, toh yanzu waye Boko Haram har gwamna ma ake so a kashe yanzu. Bamu taba samun irin haka ba a lokacin PDP.
” Yanzu ai jiki magayi, kowa ya ji a jikin sa, harkokin kasuwanci sun ruguje, talauci ya dabaibaye kowa, ita kanta rashawa din an yi nitso a cikin ta a mulkin APC.
” Mun ga yadda APC ke mulki, ada mun yi kuskure amma ai jiki magayi yanzu kowa na ji. Ko mu a jihar Bauchi, son yin dashe karfi da yaji ne ya samu muka kwace jihar, haka a jihar Adamawa, ga kuma Zamfara. Yanzu kuma kowa ya ga yadda aka yi a jihar Edo.
Yanzu ace wai jam’iyya ta kasa nada wanda zai jagorance ta sai wani gwamna ya daukar da kansa ada lokacin ta. Hakan ya nuna tun farko gurguwa ce.
A karshe Gwamna Bala ya yabawa shugaban Kasa Muhammadu Buhari sannan ya roki shi da ya karkata akalar farautar masu cin rasahawa a mulkin sa domin hukunta su.
Sannan kuma ya ce tabbas zai jam’iyyar PDP za ta ci gaba da bashi hjadin kai domin samun nasara a mulkin sa.