An kashe Soja biyu da Boko Haram masu yawa a fatattakar Boko Haram a Magumeri

0

Majiya mai tushe daga cikin jami’an tsaro sun tabbatar da kisan soja biyu, wata maijego da kuma Boko Haram masu yawa, a gumurzun hana Boko Haram yin galaba a garin Magumeri na cikin Jihar Barno.

Majiya ta kara da cewa Boko Haram sun yi kokarin kewaye garin Magumeri da yammacin ranar Talata, inda suka rika kai hare-hare a kauyukan da ke gefen garin.

Zaratan Sojoji na Musamman a karkashin jagorancin Kwamanda Manjo Manga, su ne su ka ceto garin da mutanen sa, daga mummunan kisan da Boko Haram suka yi niyyar kaddamarwa.

“Dakaru Najeriya sun tari gaban Boko Haram suka rika musayar ruwan wuta, har suka ci galabar ‘yan ta’addar, aka kwato motar harba roka a hannun su da wasu manyan makamai masu yawa.”

“Mun yi rashin soja biyu a yayin gumurzun kuma wani daya ya ji ciwo.” Inji majiyar mu.

Wata majiya kuma ta cecko kafin sojoji su kai dauki, tuni Boko Haram sun banka wa wani asibitii wuta, ya kone kurmus.

Asibitin dai kwanan nan gwamnatin Jihar Barno ta gina shi, kuma aka bude shi.

An ce Boko Haram sun arce da wata motar tarakta wadda gwamnatin Barno ta bai wa Karamar Hukumar Magumeri kwanan nan.

Majiya kuma ta ce wata maijego ta gamu da ajalin ta, yayin da wani harsashi ya kuskure ya same ta.

Boko Haram A Kukawa

Majiya ta ce farmakin da ake cewa an kai a Kukawa, ya zo daidai lokacin da aka kai na Kukawa.

Kukawa na karkashin Baga inda aka kai wa Gwamna Babagana Zulum Hari makonni uku da suka gabata.

Majiyar cikin jami’an tsaro ta ce tabbas an kai mummunan hari a garin Kukawa, amma duk wani bayani bayan wannan, ji-ta-ji-ta ce, ba a tabbatar ba da abin da ya faru bayan nan.

“Mun san an kashe mutane da yawa. Amma ba mu da cikakken bayani. Maganar cewa Boko Haram sun kwace garin, har sun kafa tuta, ji-ta-ji-ta ce, ba mu tabbatar ba.” Inji majiyar.

Amma kuma Sahara Reporters da Daily Trust sun buga labarin cewa Boko Haram sun kama garin Kukawa, kuma sun yi garkuwa da mutane daruruwa.

Trust ta ruwaito Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ce Boko Haram sun kama garin Kukawa ranar Talata da dare, bayan al’ummar garin sun koma da zama garin.

Mazauna Kukawa sun shafe shekaru biyu su na zaman gudun hijira a sansani. Boko Haram sun mamaye garin bayan mutanen garin sun koma da zama, ba da dadewa ba.

Share.

game da Author