An gargadi ‘yan Najeriya kada su ci wani kurungun kifi mai suna fugu, wanda naman sa ke kisa

0

An gargadi ‘yan Najeriya su kaurace kuma kada su kuskura su ci wani kurungun kifi mai suna fugu, wanda a Turance ake kira ‘pufferfish’, domin naman sa ya na kisa.

Mataimakin Daraktan Noman Kifaye na Hukumar Babban Birnin Tarayya, Abuja, Jonah Dabit ne ya yi wannan gargadin a cikin wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES a ranar Litinin.

Wannan kifi mai suna pufferfish, an fi samun sa a kasar Japan da sauran cikin tekun kusa da kasashe irin Najeriya.

Sannan kuma ya na da jinsi daban-daban da suka hada ‘toadfish’, ‘globefish’, ‘blowfish’, balloonfish’, ‘bubble fish’, swellfish’ da sauran su da dama.

Rahotanni sun ce akwai jinsin wannan kurungun kifi sama da 120 a duniya.

Akasarin jinsin wadannan kifaye akwai guba a cikin naman su. Kuma su na daga cikin jinsinan kifayen da naman su ke kisa farat-daya a duniya.

A cikin hantar su ko hanjin su fa tsokar jikin su akwai sinadarin gubar ‘tetrodotoxin’, mai kisa farat-daya.

A kan ga alamun illar cin kifin a jikin mutum a fuskar sa idan ta kumbura, haka a baki da harshe duk za a ga dafin gubar bayan minti 30 zuwa awowi shida bayan cin naman kifin.

Daga nan sai alamomin ciwon kai, jiri, magana da kyar, gudawa da kuma amai da kasalar jiki.

Daga nan sai sauran jiki ya shanye, sai mutuwa bayan huhu da hantar mutum sun daina bugawa.

Cikin 2015 PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda wasu mutum biyu suka ci naman kifi suka mutu a Jihar Ebonyi, kifin kuma mai guba ne.

Irin wannan kifi ya yi kisan mutum 131 a Chana cikin 2004, haka ya kashe mutum 128 a Taiwan cikin 2012.

A kasashen Amurka da Bangladesh ma wannan kifi mai guba ya yi kisa.

Da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES, Dabit ya ce wannan kifi hatsari ne sosai domin akwai guba mai karfi a jikin sa.

Ya ce mazauna Lagos da ke bakin ruwa su yi hattara. Kuma ya ce za a iya samun kifin har a ruwan Adamawa, Taraba, Lokoja da Kebbi da yankuna irin Neja.

“Wasu don ganganci suna ci. Wasu masunta kuma sun san shi, sun kuma san illar sa.” Inji shi.

Share.

game da Author