Mafi yawan wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ba su da wata mu’amala da kusanci da wanda ya fita kasar waje, ko wata jiha ko kusanci da mai cutar Coronavirus. Hakan ya na nufin akasarin wadanda suka kamu a Najeriya, ba su san ta yadda aka yi suka kamu ba.
Wannan na cikin rahoton watan Agusta da Hukumar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC) ta fitar a ranar Lahadin a Abuja.
Duk da raguwar yawan rahotannin adadin masu kamuwa da cutar Coronavirus ke yi a kullum a yanzu, har yau akwai fargabar cewa sake bude harkokin komai a kasar nan a yanzu zai iya zama sammakon-bubukuwa.
Ranar Lahadin an bayyana mutum 3O4 sun kamu da cutar, adadin da ya fi na sauran kwanakin tsawon makonni biyu a here. Tun daga ranar Juma’a da ta gabata, adadin da ake samu sun kamu ba su kai 500 a kowace rana.
Adadin baya-bayan nan ya nuna an samu mutum 43,341 suka kamu a Najeriya.
Abu Mai Daure Kai:
NCDC ta ce abin da ke daure kai shi ne kashi fiye da 70%, wato mutum 31,237 duk ba a san yadda aka yi suka kamu ba. Kuma ba a san wanda ya kamu da cutar suka dauka daga gare shi ba.
An dai hasashen ko sun dauka ne daga iyalan su, abokan aiki ko kuma makwautan su.
Hakan ya ce ya kawo matsala wajen bincike da bin-diddigin inda suka dauki cutar, domin akasarin su ba su fita kasa ko Jihar da cutar ta fantsama ba, kuma ba su fita sun shiga cikin tirmitsitsin jama’ar da aka iya samun wadanda ke dauke da cutar ba.
Ya zuwa lokacin da ake rubuta wannan rahoto, mutum 287, 582 kacal aka yi wa gwaji a Najeriya, a cikin al’ummar da ta kai milyan 200.
Cutar Ta Fi Kama Maza Fiye Da Mata: Rahoto ya nuna zuwa yanzu a Najeriya, Korona ta Kama namiji 28,305, kuma 15,536. Wato kashi 65% mata kuma kashi 35%.
Kashi 25% da suka kamu sun kama daga shekaru 31 zuwa 40. Daga cikin mutum 43,841 da suka kamu, mutum 20,308 sun murmure a jihohin kasar nan 36 da Abuja, har an sallame su zuwa gida. Zuwa ranar Lahadi Coronavirus ta kashe mutum 888 a Najeriya.