Masana kimiyyar lafiyar Ƙwaƙwalwa sun ce ƙwaƙwalwa bangaren jiki ne da ke da matuƙar mahimmanci wajen gudanar da kai komo a jikin Ɗan Adam.
Likitoci da ita kanta ƙungiya kiwon lafiya ta Duniya sun bayyana cewa akwai wasu ɗabiu da mutane ke yi da ke lalata ƙwaƙwalwa sannan da rage kaifin sa.
1. Rashin Cin Abinci Da Safe
Rashin cin abinci da safe na cikin hanyoyin dake dakusar da kaifin kwakwalwar mutum.
Abinci na dauke da sinadarin dake inganta aikin kwakwalwa inda haka ke taimaka wa mutum wajen fahimtar abubuwa.
2. Damuwa da Yawan Fushi
Yawan damuwa da saurin yin fushi musamman akan abin da bai taka kara ya karya ba na cutar da ƙwaƙwalwa.
Yawan damuwa da yawan fushi na cutar da kiwon lafiyar mutum domin Suna haddasa cututtuka dake kama zuciya, tabuwan hankali, mantuwa da sauran su.
3. Shan Taba Sigari
Shan taba Sigari na mantuwa domin hayakin taban da ake zuka na cutar da kwakwalwa.
Sannan taba na cutar da huhun mutum.
4. Shaƙar Gurbataccen Iska
Kwakwalwar mutum na bukatan iska wanda ake kira ‘Oxygen’ da turanci domin gudanar da aiyukkan da ya kamata.
Rashin samun wannan iska kuwa na dakushe kaifin kwakwalwa.
5. Yin Barci Da Hula Ko Ɗankwali a Kai
Daura dankwali ko saka hula na hana kwakwalwa samun iskan da yake butaka domin gudanar da aiki da huta wan da ya kamata ya samu.
6. Yawaita Shan Kayan Zaki
Zaki na taimakawa wajen kaifafa zurfin tunani Sai dai likitoci sun ce yawan shan sa na cutar da kwakwalwa.
7. Rashin Samun Isasshen Barci
Rashin yin barci a lokacin da ya kamata kuma na tsawon lokacin da ya kamata na cutar da ƙwaƙwalwa da kiwon lafiyar mutum.
Likitoci sun ce kamata ya yi mutum ya samu barci na tsawon awa takwas duk rana domin kaifafa ƙwaƙwalwa
8. Yin Aiki A Lokacin Da Mutum Bashi Da Lafiya
Yin aiki lokacin da mutum ke fama da rashin lafiya na cutar da ƙwaƙwalwar sa domin a wannan lokaci jikin mutum hutu yake bukata.
9. Rashin Kuzari
Rashin walwala, rashin yin magana na cutar da ƙwaƙwalwar mutum ya kebe wuri ɗaya shiru
10. Yawan Cika Ciki Da Abinci
Narka wa ciki abinci nak na jagula ƙwaƙwalwa. Ya kan rake kaifin sa.
11. Kure Ƙaran Sauti a Kunne
Saka na’urar jin sauti a kunne sannan a kure shi na jagwalgwalawa natsuwar ƙwaƙwalwar mutum.
Discussion about this post