8-2: Tonon Silili 10 da Bayern Munich ta yi wa Barcelona

0

Ragargazar da Kungiyar Kwallon Kafa ta Bayern Munich ta yi wa Kungiyar Barcelona a ranar Juma’a, zai zame wa kulob din fatalwa, kurwa da wobuwar da har abada ba za a manta a duniyar tarihin kwallon kafa ba.

An rika sheka wa Barcelona kwallaye kamar yadda ma’auni ke kamfatar gero ko masara a ma’auna, a tsakiyar kasuwa ya na shekawa a cikin buhu.

Ga kadan daga cikin abubuwan tonon sililin da wannan tsarki da ruwan barkonon da aka yi wa Barcelona ya fito da su a fili.

1. Rabon da a jefawa wa Barcelona kwallaye har 8 a raga, bana shekara 73 kenan. Wato tun cikin 1946 da kungiyar Sevilla ta zabga mata kwallaye 8:0 a gasar cin Kofin Copa Del Rey.

2. A tarihin Champions League babu wani kulob da aka taba zabga wa kwallaye 8 girmis, sai Barcelona.

3. An yi wa Barcelona tsarki da tafasasshen ruwan barkono a lokacin da dan wasan da aka fi ji da shi a duniyar kwallo, Leonel Messi shi ne kaftin din kulob din.

4. Kalmar ‘takwas’ ko kidayar 8 ta zame wa Barcelona abin bakin ciki da firgici, watakila har a daina yayin kwallo a duniya, idan ma za a daina din. Ga dalilai:

a) An ci Barcelona kwallaye 8, bayan watanni 8 da daukar kociyan su Quique Setien aiki.

b) An ci Barcelona kwallaye 8 a cikin watan 8.

c) An zabga wa Barcelona kwallaye 8 a wasan da aka yi karfe 8 na dare.

d) An zabga wa Barcelona kwallaye 8 a kasar Portugal, kasar da sunan ta haruffa 8 ne (P.O.R.T.U.G.A.L).

e) Shekaru 8 kenan rabon da a ce Barcelona ta dana tarko a La Liga, Supa Cup, Champions League da sauran gasanni, amma ba ta kama ko da gurguwar gafiya ko balbela ba.

5. A karon farko an yi wasa an tashi masu nazarin takun kwallon kafa ba su bai wa Leonel Messi ko da maki daya ba.

6. Tun a lokacin da Barcelona ta dauko Setien, sai da PREMIUM TIMES HAUSA ta buga dogon nazarin cewa Barcelona ta yi cinikin-biri-a-sama.

7. Shekarar 2020 ta fara nuna karyewar alkadarin Barcelona tun a wasannin La Liga biyu da ta buga da Real Madrid a gida da waje.

2019/2020 ce Kakar La Ligar da Barcelona ta kasa jefa ko da kwallo daya a ragar Real Madrid. Rabon da haka ta faru kuwa, tun cikin 1999/2000, shekaru 20 da suka gabata.

8. Barcelona ne kulob din da a tarihin Champions League aka fitar da ita da yawan kwallaye 18 da aka zabga mata a wasannin siri-daya-kwale na shekara uku a jere.

2018 Roma ta lallasa Barcelona da cin kwallaye 4:0, cikin 2019 Liverpool ta yi mata 4:0. Sai yanzu kuma cikin 2020 Bayern Munich ta zurara mata kwallaye 8. Idan an hada, kwallaye 16 kenan.

9. Tun a hutun-rabin-lokaci Messi ya karaya. Shi ya sa ya kasance kamar akuyar da ruwan sama ya yi wa dukan tsiya.

10. Burbushin magoya bayan Barcelona sun tarbe su a otal din da suka sauka a birnin Lisbon na Portugal, suka rika aibata su, su na yi masu ba’a da shegantaka saboda haushi, har su na yi ce musu, “cas kurage, cas kuregu! Cas kurege, cas kuregu!”

Share.

game da Author