2023: Babu tsarin karɓa-karɓa a APC, kowa zai iya takarar shugaban ƙasa daga kowanni yankin Ƙasar nan – Kalu

0

Bulaliyar majalisar Dattawa, kuma tsohon gwamnan Jihar Abia, Orji Uzoh Kalu ya bayyana cewa jam’iyyar APC bata yi shirya tsarin karɓa-karɓa a shugabancin Najeriya ba, saboda haka kowa zai iya fitowa takara a 2023 daga kowanne yankin ƙasar nan.

Kalu ya faɗi haka ne bayan ziyara da ya kai wa tsoffin shugabannin ƙasar nan a garin Minna, Ibrahim Babangida da Abdussalami Abubakar. Sannan ya ƙara da cewa zai yi shugabancin Najeriya yadda ya za samu cigaba idan aka bashi wannan dama.

“Yanzu dai in majalisar Dattawa, kuma zan sake neman kujerar idan wa’adina ta zangon farko ya kare. Amma kuma idan mutane na suka bukaci in yi takarar shugabancin Najeriya, zan fito ko shakka babu.

” Babu wani tsari na karɓa-karɓa a jam’iyyar APC, kowa zai iya fitowa takara ya nemi duk kujerar daga ko wani yankin ƙasar nan.

Game da matsalar tsaro da ake fama da shi a ƙasar nan, Kalu ya ce akwai makarƙashiya da ake yi.

” Akwai maƙarƙashiya da ake yi wa bangaren tsaro a ƙasar nan. Kuma ina tabbatar muku cewa zamu kawo ƙarshen wannan zagon ƙasa da ake yi wa bangaren tsaron ƙasar nan amma kusa ni tabbas mun gano haka.

Shi dai Kalu na daga cikin kalilan din ƴan ƙabilar Igbo da suke jam’iyyar APC, kuma hakan bai hana a daure shi ba a dalilin zargin yin sama da faɗi da yayi da kuɗin jihar Abia a lokacin da yake gwamnan jihar.

Share.

game da Author