ƳAR FARA TA NUNA: Dalilin da yasa akayi kutun-kutun din ganin El-Rufai bai halarci taron NBA ba, Daga Mohammed Mohammed

0

A tashin farko dai gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai bai nemi dole a saka shi cikin wadanda za su yi jawabi a taron Ƙungiyar Lauyoyi Na kasa ba, su da kan su suka gayyace shi kuma suka bashi maudu’in da zai yi magana akai.

Ashe Ashe akwai wadanda basu ji dadin wannan gayyata ba saboda kowa yasan El-Rufai gwarzon namiji ne da baya shakkan kowa wajen tsage gaskiya komai ɗacinta.

Wasu daga cikin batutuwan da za a tattauna wanda muka ji a ranar Alhamis daga bakin mataimakin shugaban Kasa, sun haɗa da halin da ake ciki game da rikicin Kudancin Kaduna.

Mataimakin Shugaban kasa yayi dogon jawabi akai, amma kuma a ganina ai idan har maganar rikicin kudancin Kaduna zai taso ko kuma za a tattauna shi a wannan taro babu wanda ya fi dacewa ya yi bayani a akai irin gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Dalili kuwa shine, na daya dai shine gwamnan da yafi jajircewa wajen ganin an kawo karshen wannan tashin hankali a yankin Kudancin Kaduna.

Tun bayan darewar sa kujerar mulki jihar Kaduna yake ta fadi tashi don ganin an dakatar da aikata ta’addanci a yankin da wasu sassan jihar da ta’addanci yayi tsanani.

Sai dai kash, mutanen yankin kamar yadda ya bayyana, basu amince da tsarin haka ba, duk da cewa ba shi kadai ba yayi fama da mutanen yankin ba, a lokacin da ɗan uwansu wanda ɗan asalin yankin ne, Ibrahim Yakowa ya zama gwamna, shi ma bai ji da daɗi ba, sau da yawa har jifan sa sukan yi cewa baya musu abinda suke so a yankin Kudancin Kadunan. Shima Ramalan Yero haka yayi wannan fama, duk da basu taka wani rawar gani ba sai yanzu da El-Rufai yake huɓɓasan ganin wannan matsala ya kau amma kuma an saka shi a gaba.

Baya ga kokarin kafa sabbin sansanonin jami’an tsaro da gwamnan tare da haɗin guiwar gwamnatin tarayya a yankin a kullum yana ganawa ne da kungiyoyin da basu jituwa da juna a yankin domin a samu sulhu a tsakanin su a zauna lafiya, amma ina ruwan ka da mai bakar aniya, duk ba zai ga haka tunda ba hakan yake so ba.

Idan yau ƴan kabilar kudancin Kaduna suka kai wa Fulani da shanun sa hari, bayan kwana uku suma sai su afka musu. Haka dai kullum. Amma kuma ɓangare ɗaya ne ke fantsama ihu a kullum shi fa ana kashe, gwamnati bata komai akai.

Irin wannan taro na NBA ne ya kamata gwamna El-Rufai ya halarta domin fasa kwan ga kowa duk duniya a san gaskiya a kuma san abinda jihar ke yi domin kawo karshen rikicin.

Amma sai a fake da wai wasu basu son ya halarta shi yasa ba za a barshi ya bayyana ba a ka soke gayyatar.

Ina adalci da gaskiya a cikin haka. Idan ba kazo ka bi diddigin abinda ke faruwa bane sannan ka shiga wadannan yankuna, ba za ka san ko menene ainihin abinda ke faruwa ba.

Ya dai tabbata karara cewa filine ba a so a aba El-Rufai a taron NBA, kada ya fasa kwan, ya tona wa wasu asiri sannan ya fede gaskiyar abinda ke faruwa a yankin kudancin Kaduna da jihar baki daya duk duniya su sani akayi kutun-kutun aka kirkiro wasu dalilai da basu da tushe aka yi amfani dasu wajen soke gayyatar da aka yi masa. Idan ba tsoro ba a bashi fili mana ya yi magana, da wasu sun kasa barci, har da masu ci da addini. Kuma wai sai gashi ana tattauna batun a taron.

Share.

game da Author