Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za a fara rubuta jarabawar kammala babban Sakandare daga ranar 4 ga watan Agusta zuwa 5 ga watan Satumba.
Gwamnati ta ce da zarar an kammala wannan jarabawa sai kuma a maida hankali wajen yin jarabawar NABTEB da NECO.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta umarci ;yan aji shida na babban sakandare su koma makaranta domin shirin rubuta jarabawar WAEC.