Hukumar UNODC dake karkashin majalisar dnkin duniya ta gargadi mutanen kasashen duniya da gwamnatoci, su rika sara suna duban bakin gatari da kuma jan kunnen mutane game da nisanta daga yin mua’mula da tsuntsaye da namun daji.
Hukumar ta yi wannan kira ne a taron gabatar da rahoton illar dake tattare da farautar namun daji na shekarar 2020 da aka yi a Abuja.
Rahotan ya nuna cewa Kashi 75 bisa 100 na cututtukan da ake fama da su a duniya na da alaka da cin namun daji.
Rahoton ya Kuma nuna cewa cutar SARS-CoV-2 Wanda ya haifar da cutar coronavirus na da alaka da wata dabban daji mai suna pangolins.
“Cin irin wadannan dabba ba shi da alfanu matuka.
Bayan haka rahotan ya gano kasashe 140 da Suka shahara a kasuwancin Pangolins dake kawo cutar coronavirus.
Binciken ya nuna cewa kasuwar siyar da fatar wannan dabba ya Karu zuwa ninki 10 tsakanin shekaru 2014 zuwa 2018.
Sannan Najeriya na cikin kasashen duniyan da Suka taka mahimmiyar rawa wajen habbakar kasuwancin namun daji a nahiyar Afrika.
A yanzu haka kawai kasashen 150 da Suka shahara wajen farauta da siyarwa da safara namun daji dabam dabam a fadin duniya.
Shugaban UNODC Ghada Waly, kwamishinan EU Jutta Urpilainen da shugaban ‘Convention on International Trade in Endangered Species of Wild Fauna and Flora (CITES)’ Ivonne Higuero sun Yi Kira ga kasashen duniya da su gaggauta daukan matakan da za su taimaka wajen hana farautar namun daji domin kare muhalli, dabbobin daji da kiwon lafiyar mutane a duniya.
Idan ba a manta ba a ranar 1 ga watan Yuli ne Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa yanzu ne duniya za ta afka cikin balbalin bala’in Coronavirus cewa baya ba a ga komai ba tukunna.
Shugaban WHO, Tedros Ghebreyesus ya ce matsawar gwamnatocin kasashen duniya ba su gaggauta tashi tsaye sun yi da gaske ba, to wannan cuta za ta yi wa duniya rundugun da ya wuce wanda ake ciki a yanzu fiye da kima.