‘Yan kwangila na bin Majalisa bashin kudin motocin bilyoyin nairori tun cikin 2017

0

‘Yan kwangila na zargin Majalisar Tarayya a karkashin tsohon Shugaban Ma’aikata Mohammed Sani-Omolori da laifin rike musu bilyoyin kudaden da suka sayar wa ‘yan Majalisar Tarayya motoci, tun a cikin 2017, amma har yau ba a biya su bilyoyin kudaden su ba.

‘Yan kwangilar sun kunshi kamfanoni 13, wadanda suka bayar da motoci samfurin Fijo 508, Special Edition, wadanda aka raba wa ‘yan Majalisar Tarayya, da kuma samfurin Hilux 13.

Sun yi barazanar garzayawa kotu, matsawar ba a biya su kudin su ba a cikin kwanaki bakwai.

Tara daga cikin kamfanoni sun sayar wa majalisa motoci 132, wasu kamfanoni biyu kuma sun sayar musu da motoci 18 na Toyota Hilux. Wasu kamfanoni biyu kuma sun sayar musu da kayan ofis.

A yanzu dai sun bai wa Majalisa wa’adin kwana bakwai su biya su, ko kuma su kwashi ‘yan kallo a kotu.

Wata wasika da ta fito daga ofishin lauyan su, wato Otaru Otaru & Co, wadda kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Majalisar Kasa ta amshi kwafen wasikar, ya ce an sayar da Fijo 508 samfurin 2017 a shekarar 2017 kan kudi naira milyan 25.5 kowace daya.

Kenan kudin Fijo kwaya 132, sun kama naira bilyan 3.4.

Sai kuma kudin Toyota Hilux 18 akan naira milyan 31.2 kowace daya, sun tashi naira milyan 561.6.

Akwai kuma naira milyan 211.2 na kayan amfanin ofis da wasu kamfanoni biyu suka sayar wa Majakisa, amma har yau ba a biya ko sisi ba.

PREMIUM TIMES ta ga kwafen takardar wasikar da aka lauyoyin suka aika wa Majalisa, kuma ta ga takardar da kamfanin Three Brothers Concept ya rubuta, ciki baya ga neman kudin sa, har ladar wahalar jekaoa-jekalar rike masa kudi ya nema a biya shi ta naira milyan 100.

Shi ma kamfanin Bunkari Motors ya nemi a biya shi ladar rike masa kudi tsawon lokaci da aka yi, ba tare da ya juya kudaden ya ci riba ba.

Yawancin masu kamfanonin sun yi magana da PREMIUM TIMES, kuma sun ce sun yi barazanar zuwa kotu, domin sun fahimci Majalisa ta kamo hanyar damfarar su ne kawai.

PREMIUM TIMES ta fahimci an fara biyan kamfanoni ‘yan kudade kalilan, tun lokacin kai motocin, amma kudaden ba su wuce cikin cokali ba.

Daraktan Yada Labarai na Majalisa, Rawlings Agada, ya ce ba shi da cikakkiyar masaniyar yadda takamaimen cinikin yake.

Share.

game da Author