Tsohon Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara ya wancakalar da jam’iyyar PDP, ya koma APC.
Dogara ya bayyana haka ne bayan ganawa da yayi da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati ranar Juma’a.
A shekarar 2018 Dogara ya fice daga jam’iyyar APC ya koma PDP, bayan rashin jituwa da ya shiga tsakanin su da gwamnan jihar a wancan lokaci.
Idan ba a manta ba tare suka hada kai da gwamnan Bauchi, Bala Mohammed , suka kada APC a jihar Bauchi.
Discussion about this post