Rundunar ‘Yan Sandan Yaki da Ta’addanci da ke Sansanin B a Maiduguri, sun bayyana ceto wasu sojojin sintiri da Boko Haram suka yi gaskuwa da su a kan hanyar Auno, ranar Litinin.
Lamarin ya faru da misalin karfe 2:48, kamar yadda jami’an da aka sanar wa lamarin suka tabbatar.
Kafin zuwan ‘yan sandan, har Boko Haram sun kashe sojojin biyu, sun yi garkuwa da wasu kuma sun kwaci motocin yaki biyu da bindigogi samfurin AK47 guda 60, tare da tulin harsasai.
Amma yayin da ‘yan sandan suka isa aka fara musayar wuta su da Boko Haram, sun kwato daya daga cikin motocin yakin biyu da kuma wasu harsasai.
A cikin wani faifan bidiyo da wannan jarida ta kalla, inda ‘yan sanda ke bada bayanin yadda suka yi gumurzu da Boko Haram, jagoran tawagar ‘yan sandan ya ce su na cikin tafiya a motar su ta sintiri kan titin zuwa Auno, sai suka ga wata motar soja an ajiye ta a kan wata hanya shararra, maras kwalta.
“Kuma mu ka ga gawar mutum a gefe. Tsammanin mu ko bam ne.” Inji jami’in dan sandan.
“Sai na ce mu fara bud-duba motar tukunna. Sai muka ga bindigogi a ciki, muka ce mu fara dauko su tukunna.”
Ya kara da cewa “mun yi tunanin kwaso makaman kenan mu koma baya, sai mu ka ga mota na cin wuta, kuma ga jirgin yaki a sama ya na shawagi a kan su.
Ya ce sun yanke wannan shawara ne don kada a bude musu wuta ta sama, domin na cikin jirgin ba su san da zuwan ‘yan sandan ba.
Garin Auno mai nisan kilomita 20 kacal daga Maiduguri, ya sha fama da farmakin Boko Haram cikin watan Fabrairu, inda Boko Haram suka banka wa matafiya sama da 30 wuta, kuma suka kone motoci 18.
Ko cikin zaman gida saboda Korona a cikin Afrilu, Boko Haram sun kashe mutum bakwai a Auno.
Kakakin Sojoji Sagir Musa da na ‘yan sanda, Frank Mba, duk sun ki cewa PREMIUM TIMES komai da aka tuntube su kafin a buga labarin.