Fitaccen mawaki, kuma jarumi a Kannywood, Nura M Inuwa ya shaida cewa muhimmin abin dake yi masa dadi a rayuwar sa da sana’ar sa shine yadda wakokin sa ke gyara dabi’un al’umma.
A hira da BBC Hausa, jarumin ya bayyana cewa, babu abinda ya fi da cewa da kuma moriya kamar ace mutum na yin abinda zai gyara al’umma.
” Na rera wakoki da dama da suka sauya tunanin mutane bisa wani abu da suke so aikata, amma kuma bayan sauraren wakar sai suka canja shawara, suka gani abinda za su aikata bai dace ba.
” Na rera wata waka da nayi mai taken ” Ga Wuri Ga Waina’ wakar na yin tambihi ne game da hadarin dake tattare da aikata kisan kai.
” Bayan wakar ta karade gari, sai wasu mutane suka kira ne sua shaida min cewa wannan waka ta ceto rayuwar wata budurwa da ta ke kokarin aikata kisan kai. Cewa bayan ta saurari kalaman wadannan wakoki sai ta canja shawara.
Haka kuma jarumin ya shaida wa BBC Hausa cewa, a wani lokaci da bam wani ya kira shi ta wayar hannu ya shaida masa cewa ya gama shiri tsaf zai banka wa matar sa saki, amma kuma ya hakura bayan jin irin kalaman ta natsu dake cikin wannan waka, sai hankalin sa ya dawo jikin sa ya hakura da yin sakin.
Haka kuma akwai wakar da nayi da ya sa wasu iyaye suka hakura da yi wa ‘yar su auren dole.
A karshe ya bayyana dalilan da ya sa ba acika ganin sa cikin finafinai ba, cewa ya dage ne ga maida hankali ga waka.
” Bana so in rika gwamutasa waka da fitowa a finafinai. Na maida hankali ne zuwa waka.
Wasu da PREMIUM TIMES HAUSA suka tattauna da su game da ko me za su ce kan mawaki Nura Inuwa, duk sun yaba masa kuma sun jinjina wa mawakin bisa wakokin tarbiya zuwa da yake yi.
Hassana Dalhat, a Kaduna ta bayyana cewa, ita ma da kanta wakokin Nura Inuwa na canja mata wasu shawarwari da ta kan dauka.
” Nura wa azi ya ke yi a wakokin sa domin nima kai na ya kan sa na canja wasu abubuwan nawa. Idan na saurari kalaman wakokin sa. Yana da zurfin tunani matuka.