Sojojin Najeriya sun sha sakin bayanai su na yin tir da jaridu cewa su na buga labarai na karairayi domin kashe guyawun aikin tsaron kasa da kawo tarnaki ga kokarin tsaron kasa da su ke yi.
To amma kuma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna cewa sojoji na fassara ma’anar ‘labaran bogi’ zuwa duk wani labarin da ba su so jama’a su sani, ko da kuwa ya tabbata cewa gaskiya ce aka buga.
Cikin watan Mayu sojoji sun zargi “wasu mutane kiri-kiri su na baza labaran karya domin su haddasa rashin jituwa da husuma tsakanin sojoji da jama’a da kuma gwamnati.”
“Su na kuma dankwafar da zukatan sojoji ta hanyar buga zarge-zargen karya da labarai na bogi.
Sojojin suka ce wannan dabi’a ta na da mummunan sakamakon abin da za ta it’s haifarwa a kasar nan.
Sai dai kuma sojojin kan su ba sau daya ba, an same su dumu-dumu da aikata abin da suke yin tir cewa ana aikata musu.
Ranar 11 Gs Yuli, PREMIUM TIMES ta buga labarin sojoji 356 za su yi ritaya saboda “aikin ya fits daga ran su.’
Sannan kuma jaridar TheCable, Punch da Global Sentinel duk sun buga wannan labari, cewa wasu sojojin da dama sun ajiye makamai sun kama gaban su ba tare da bin ka’idar ajiye aiki ba.
Ganin wadannan labarai ba su yi wa sojoji dadi ba, sai suka maida martani cewa labaran duk “na bogi” ne, kuma labarai ne “don a haddasa hukuma da rashin jituwa da masu goyon bayan Boko Haram suka kirkiro domin kashe guyawun sojojin Najeriya.”
“Sojoji 356 duk za su ajiye aiki ne salum-alum, kan ka’ida ba tare da wani korafi ba.” Inji sojojin.
“A halin yanzu ma sojojin Najeriya ba su fama da karancin jarumai, domin kwanan nan mutum 4,600 suka shiga aikin soja. Kuma da dama daga cikin su sun shiga horo na musamman domin yin yaki da ta’addanci.” Inji sanarwa daga sojoji.
Wannan sanarwa da jami’a suka karanta da ta fito daga sojoji, ta sa jama’a da dama bayyana ra’ayin su a kasa, su na goyon bayan duk abin da sojojin suka fada, sannan kuma su na fadar bakaken maganganu kan jaridu.
Har ma wani dogon rubutu wani ya yi sojoji suka buga a shafin su, ya na goyon bayan su, ya na kuma sukar jaridu.
Mai goyon bayan ya ce a yanzu sojojj har ma a daji suke kwana, su na kwanton-baunar jiran afka wa ‘yan ta’adda.
HumAngle ta ga takardun bayanai da aka sa wa hannu wadanda suka tabbatar da cewa sojojin za su yi ritaya ko sun yi ritayar saboda dalilai na “aikin soja ya gundure su.”
Takardun bayanai da ke dauke da ranar 8 Ga Yuli, na dauke kuma da sunayen sojojin da aka amince za su ajiye aiki a farkon 2020.
Su 380 ne, kuma wani Burgediya Janar Gagariga ne ya sa hannu kan takardun, a madadin Babban Hafsan Sojojin Najeriya.
Jerin sunayen na dauke da mukamin kowane soja, sunan sa, lambar dauka aikin soja, inda ya ke aiki da kuma dalilin ritayar sa.
Yayin da 24 daga cikin su sun ce sun aniyet aiki domin karbar sarautar gargajiya, sauran duk sun nuna cewa “aikin ne ya gundure su.”
Wannan kuma ba shi ne na farkon abinda aka buga ya faru a cikin sojoji su kuma su karyata ba.
Cikin Afrilu, sun bayyana wani labari da aka buga cewa na “bogi” ne.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa sojoji sun dakatar da damar bada sararin a yi ritaya haka kawai. A ranar da aka buga labarin sai sojoji suka karyata a shafin su na twitter.
Daga baya ita kuma PREMIUM TIMES da ta ga haka, sai ta buga shafin kwafen takardar da sojoji suka fitar da bayanan dakatarwar .
Discussion about this post