Yadda ramcen da babu kudin-ruwa na CBN zai habbaka Shirin Bunkasa Harkokin Kudaden Masu Kananan Sana’o’i -Majalisar Musulunci

0

Majalisar Kolin Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) da ake kira Nigerian Council of IsIamic Affairs, ta yaba wa shirin bayar da ramcen da babu kudin-ruwa, wanda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya shigo da shi.

A cikin wata sanarwa da NSCIA ta fitar a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar, na Sokoto, ya ce wannan shirin bayar da lamuni ya shafi Shirin Bayar da Lamunin Noma (Anchor Borrowers Programme, ABP), Harkokin Kasuwancin Noma, Shirin Bunkasa Kanana da Matsakaitan Harkokin Zuba Jari, sai kuma Tsarin Lamunin Inganta Harkokin Lafiya d sauran su.

Sanarwar wadda Mataimakin Sakatare na NSCIA, Salisu Shehu ya sa wa hannu, ya yi tsinkayen cewa wannan shiri alheri ne matuka, kuma zai yi tasirin bunkasa harkokin tasarifin kudade, ta yadda zai taimaka a kauce wa barazanar kuncin tattalin arzikin kasa da ke kokarin karya kofa ya kutsu cikin Najeriya sakamakon barkewar annobar Coronavirus.

NSCIA ta ce Bankin CBN ya fito da ka’idoji da sharudda da kuma karin haske dalla-dalla na wannan lamuni na ramcen kudade ba tare da dora kudin-ruwa ba.

Yayin da ita wannan Majalisar Harkokin Musulunci ke addu’a Allah ya sa wannan shiri na CBN ya yi gamo-da-katar din gagarimar nasara, Majalisar ta kuma jinjina wa CBN da Gwamnatin Tarayya da suka shigo da wannan kassitaccen shiri.

“Tsawon shekaru da yawa an mayar da musulmin kasar nan saniyar-ware a bangaren harkoki da hada-hadar kudade da sauran tsare-tsaren bunkasa harkokin kudaden da CBN ke bijirowa da su, saboda kawai wata boyayyar manufar da masu kirkiro shirin ke da ita.” Inji sanarwar NSCIA din.

“Ga Musulmi wadanda suka kunshi sama da rabin al’ummar kasar nan, kaucewa hada-hadar kudaden da babu kudin-ruwa a ciki, abu ne da ke da tushe da asali a cikin addinin su. Kuma akasarin su sun gwammnace rayuwa cikin fatara da talauci da a ce su rika karba ko bayar da kudin-ruwa, sannan su hadu da fushin Mahaliccin su.

“To amma wannan tsari da babu kudin-ruwa a cikin sa, tsarin zai bunkasa Shirin Inganta Hada-hadar Kudade a cikin dimbin Musulmin kasar nan da kusan kashi 60% bisa 100% a cikin yawancin al’ummar yankuna da dama a garuruwan da Musulmi ke da rinjaye.

“Bincike ya nuna cewa matsawar CBN bai shigo da tsarin bayar da ramce ba da kudin ruwa ba, to babu yadda yadda za a yi ya samu nasarar kashi 80% bisa 100% na kudirin da ya ke son cimma ba cikin al’ummar Musulmi ba a cikin 2020. Ta haka ne kawai yunkurin bunkasa masu kananan karfin kasuwanci da noma da CBN ke yi zai samu gagarimar nasara.”

Mai Alfarmar Sarkin Musulmi ya kuma jaddada cewa zai umarci dukkan Sarakunan Musulunci su shiga wayar wa jama’a kai dangane da fa’ida da muhimmancin wannan shiri.

NSCIA ta kuma yi kira ga dukkan ‘yan Najeriya da su rungumi wannan shiri hannu bib-biyu.

Share.

game da Author