Yadda Minista Malami ya karya doka, ya buga gwanjon kayan satar da EFCC ta kama – Magu

0

Irin yadda dakataccen Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya karkato akala shi ma ya na sheka ruwan zargin harkalla kan Ministan Shari’a Abubakar Malami, zargin a yanzu kuma ya sake fallasa yadda Malami ya gurgunta kokarin da EFCC ta yi domin tabbatar da an yi gwanjon danyen mai na sata da tankokin jiragen ruwan da aka loda man ta hanyar da doka ta gindaya yin gwanjon kayan sata.

Magu da ke amsa tambayoyin Kwamitin Bincike kan zargin yin sata-ta-saci-sata, ya shaida wa Kwamitin Ayo Salami yadda Malami ya rika shirya timirmirar yin gwanjon tankoki da danyen man, ta yadda ya janyo asarar naira milyan 283 ga kasar nan.

Malami: Malam Ko ‘Malam Mai Rugumutsi?:

Magu ya na nufin Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ne kanwa-uwar-gamin kutunguilar janyo wa Najeriya asarar daya daga cikin tankokin danyen man fetur, wadda ke dauke da metrik tan na danyen mai 1,459 (daidai da lita 1,979,056.45).

Magu ya yi wannan zargin ne lokacin da ya ke amsa tambayoyin zargin cewa EFCC a karkashin sa ta rika yin sata-ta-saci-sata a kan kayan satar da aka kwato daga hannun barayin gwamnati da sauran mazambata, ciki kuwa har da tankokin jiragen ruwan da EFCC ta kama makare da danyen mai na sata.

Yayin da Magu ke bayanin yadda aka ‘yar-wala-wala da wata dankareriyar tankar jirgin ruwa mai suna MT Good Success, Magu ya ce an kwace tankar jirgin ruwa a lokacin da ta ke dauke da metrik tan 1459 na danyen man fetur.

“Sannan kuma EFCC ta kulle asusun kamfanin da ke da tankar, wanda ke bankin FCMB mai cike da kudi naira milyan 66,069,505 da kuma dala 975,694.50.”

Magu ya ce sunan kamfanin Hepa Global Energy Limited, kuma su ke da tankar daukar danyen mai MT Good Success.

Ya ce duk da kokarin da kamfanin ya yi domin wata kotu ta soke hukuncin da Mai Shari’a O.E Abang ya yanke, wanda ya bai wa EFCC ikon kwace dankareren jirgin ruwan da kuma danyen man da ke ciki har da asusun kamfanin, a Kotun Daukaka Kara.

Magu ya ce kafin Kotun Daukaka Kara ta bada umarnin janye kwace jirgin da janye kulle asusun na banki, tuni har ya fara shirye-shiryen ganin Gwamnatin Tarayya ta amfana da kudaden da ya kwato na kamfanin, ta hanyar loda su cikin Asusun Gwamnatin Tarayya da ke Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ga shaidar wasikar da na aika wa Malami -Magu:

Magu ya ce ya aika wa Minista Malami wasika mai Lambar Adireshi EFCC/SC/JUS/07/101. Ya aika wasikar a ranar 24 Ga Maris, 2016.

Abinda Wasikar Ta Kunsa: SANARWAR A YI GWANJO, wasikar ta na bukatar a yi gwanjon jirgin ruwan tare da zayyana ka’idojin da za a bi wajen yin gwanjon.

Magu ya ce har yau Ministan Shari’a Malami bai maida masa amsa ba.

Kakudubar Yadda Jirgin Ruwa ya nutse a cikin aljihu:

Magu ya ci gaba da bayani: “Ranar 10 da kuma 23 Ga Nuwamba, sai Rundunar Sojojin Ruwa (wadda ke tsare da jiragen ruwan da EFCC din ta kwace), ta rubuto wa EFCC wasika cewa dankareren jirgin ruwa na MT Good Success ya nutse a cikin ruwan teku.

“Sojojin Ruwa suka ce mana cewa jirgin ya fara nutsewa, tun ana hangen sa kuma aka bi aka kokarin damko shi tun daga Tashar Yi Wa Jiragen Ruwa Waigi ta Lagos, har dai jirgin ya nutse, kuma aka yi ta lalube a ruwa amma ba ci karo da shi ba.”

Sojojin Ruwa suka ce kuma dama muddin jirgin ruwa ya fara nutsewa, to kamfanin Julius Berger ne kadai ke da kayan aikin iya janyo shi kafin ya nutse karkashin teku.

Magu ya ce ganin yadda aka ce jirgin ruwa sukutum ya nutse, shi ne sai suka bada shawarar a yi gwanjon sauran da suka rage.

“An rubuta wasika ga Pinnacle Trading Company and Investment Nageria Limited domin su yi gwanjon jirgin ruwan da abin da ke ciki.

Ya ce amma daga baya EFCC ta gano ashe an karya dokar kwangika ta 2007, kuma hukumar ta soke bayar da gwanjon tankar jirgin ga Pinnacle, tare da yin sanarwa a kafafe.

Magu ya ce EFCC ta yi haka bayan ta gano cewa da kamfanin Pinnacle Limited da Omo-Jay Limited da ake tuhuma da satar danyen mai a Neja-Delta, duk gungun mutane daya ne ke da su.

Cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES ta buga ba’asin dalilin da sa Minista Malami ta ce ya bada umarnin yin gwanjon kayan sata ga kamfanin da kotu ke tuhuma da tabka zamba da harkalla -Minista Malami.

Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya bayyana cewa umarnin da ya bayar a yi gwanjon wasu tankokin jiragen ruwa da man da ke ciki ga kamfanin da ke gaban kotu ake tuhuma da harkalla da zamba, ba aibi ba ne, domin ya bada umarnin bai kauce wa doka ba.

Malami ya yi wannan raddi ne bayan an fallasa yadda yadda yadda bada umarni a sayar da wani dimbin man fetur da gas da ke da kare cikin wasu jiragen ruwan daukar mai har hudu.

Ya bada umarnin kamfanin Omoh-J Nigera Limited ya kwashe ya kwashe mai a matsayin cinikin kayan gwanjo, duk kuwa da cewa shi ma Omoh-Jay din kotu na tuhumar sa da satar danyen mai har metrik tan 120,000 dankare a cikin tankokin jiragen ruwa.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Minista Malami, mai suna Umar Gwandu ya fitar, Malami ya ce, “umarnin a sayar da tankokin da man ya fito ne bayan kotu ta yanke huncin karshe cewa gwamnati ta kwace jiragen lodin danyen man danyen man da ke ciki, tare kuma da umarnin da Ofishin Shugaban Kasa ya bayar, a ranar 25 Ga Oktoba, 2018.

Da ya ke kare kan sa daga abin da al’ummar kasar nan ke kallon bahallatsa ce ya tabka, Malami ya ce ya yarda tabbas kotu na kan tuhumar Jerome Itepu mai tankokin jiragen daukar mai na kamfanin sa Omoh-Jay Nigeria Limited da laifin satar danyen mai, to ya kamata a lura ba a kai ga samun sa da laifi ba.

Saboda haka a cewar Malami, za a iya mu’amalar cinikayya da kamfanin, tunda ba a kai ga samun sa da laifi ba.

“Da an samu Minista Malami da karbar toshiyar baki ko kashe-mu-raba, ko hannu a cikin jarin kamfani, to shi ne zai zama abin damuwa.

Daga nan sai Malami ya bada bayanin tun asali yadda EFCC ta kama jiragen dakon man da kuma tsawon lokacin da kamfanin ya dauka su na kotu, shi da EFCC.

Haka Malami ya rika yanko bayanai daga wasu takardun bayanan da hukumomin da abin ya shafa suka rika fitarwa dangane da rikicin tankokin jiragen ruwan da kuma man, wanda aka kama tun a lokacin mulki Goodluck Jonathan.

Yadda Malami ya kara yi wa Kamfanin ‘Yan Harkalla, Omo-Jay gwanjon Jiragen Ruwa -Magu

Magu ya ce abin al’ajabi da mamaki shi ne yadda a gefe daya EFCC ta gurfanar da Omo-Jay bisa harkallar satar danyen mai, a daya gefen kuma Malami ya bada umarnin a yi musu gwanjon jiragen ruwan gaba daya.

Hakan a cewar Magu, Malami ya yi ne alhalin ya yi watsi da wasikar da EFCC ta aika masa cewa sun sami umarni daga kotu EFCC ta hana a rike jiragen.

Magu duk ya hada wa Kwamitin Bincike wasikar da ya aika wa Minista Malami da kuma kwafen umarnin da Malami ya bayar cewa a sayar wa kamfanin ‘yan harkalla gwanjon jiragen da danyen man da ke ciki.

Magu ya ce ya yi mamakin yadda sai dai labari kawai ya ji an hada baki da Rundunar Sojojin Ruwa da Minista Malami an fara hada-hadar gwanjon jiragen da danyen man da ke ciki.

Ya shaida wa kwamiti cewa ya sanar da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo irin kokarin da ya yi domin ganin ba a yi gwanjon ba, amma bai yi nasara ba.

PREMIUM TIMES ta yi kokarin jin ta bakin Malami kafin a buga wannan labari. Amma an buga wayar sa, bai amsa ba.

Share.

game da Author