Dakataccen Shugaban EFCC Ibrahim Magu, ya bayyana cewa Ministan Harkokin Shari’a, Abubakar Malami ne ya gurgunta kokarin EFCC don ganin an maido tsohuwar Ministar Fetur, Deizani Allison-Maduekwe gida Najeriya daga gudun hijirar da ta yi.
Magu ya shaida wa Kwamitin Bincike cewa karya Malami ya yi masa da kazafi da sharri, da ya ce shi Magun ne ya gurgunta kokarin dawo da Deizani Najeriya din.
A baya Malami ya zargi Magu a rahoton da ya bai wa kwamiti cewa Magu ya ki hada kai da jami’an tsaron wasu kasashe domin a damko wa Najeriya Deizani daga Birtaniya a dawo da ita Najeriya ta fuskanci hukunci.
Tura Ta Kai Banko:
Cikin wani kwafen bayani da Magu ya yi wa Kwamitin Bincike, wanda ya fado hannun PREMIUM TIMES, magu ya ce karya kawai Malami ya shirga masa, amma shi bai ki sanar da Hukumar Hana Laifuka ta Birtaniya bayanan zarge-zargen da EFCC ke wa Deizani ba.
Magu ya rubuta wa kwamiti dalla-dallar irin kokarin da ya rika yi tare Hukumar NCA mai binciken laifuka a Birtaniya, kuma ya kawo misalan irin binciken da suka yi na hadin-guiwa da juna, cikin har da na Deizani Allison-Maduekwe.
Magu ya shaida wa Kwamitin Ayo Salami cewa ganin yadda Birtaniya ta dauki tsawon lokaci ba ta gurfanar da Deizani ba, sai EFCC ta rubuta wasika ta hannun Ministan Shari’a Malami, ta nemi Birtaniya ta damko Deizani a tasa keyar ta zuwa Najeriya domin ta amsa tuhuma a nan Najeriya.
Magu ya ce har zuwa yau din nan Malami bai sanar da EFCC amsar da mahukuntan Birtaniya suka bayar ba, dangane da wasikar da EFCC ta nemi a kamo mata Deizani a maido Najeriya.
Yadda Malami ya yana dawo da wasu barayin gwamnati baya ga Diezani – Magu
“Ba Deizani ce kadai Malami ya gurgunta kokarin dawo da ita daga kasashen waje domin su fuskanci tuhuma ba. Akwai wasu ma da na rika rubuta masa wasikar bukatar a dawo da su, wato neman a tsara kamo su, amma har yau bai ba ni amsa ba.
“Daga cikin wadanda Minista Malami ya hana a dawo da su domin fuskantar tuhuma, har da Robert John Oshodin, gogarman jidar milyoyin dalolin kudaden makamai a madadin Sambo Dasuki. Akwai kuma toshon Hadimin Shugaba Goodluck Jonathan kan Harkokin Yin Afuwa, Kingsley Kuku da wani Hima Abubakar.”
Magu ya hada da kwafe-kwafen shaidar wasikun da ya rika aika wa Malami, kuma ya ce har yau Malami bai sanar da shi dalilin da har yanzu ba a dawo da su Najeriya ba.
“EFCC ta nemi Malami ya ba ta kwafen wasu muhimman bayanai dangane da harkallar kwangilar P&ID, amma har yanzu bai bayar ba.” Duk haka Magu ya rubuta.
PREMIUM TIMES ta nemi jin ta bakin Minista Malami a safiyar Talatar nan, amma da aka kira lambar sa, bai dauka ba.
Discussion about this post