Yadda mahara suka kashe ‘yan sanda 4 dake raka motar daukan Kudi a Enugu

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta bayyana cewa mahara sun kai wa motar daukan kudi hari har sun kashe ‘yan sanda hudu daga cikin jami’an tsaron dake raka motar.

Kwamishinan ‘yan sanda Philip Maku ya sanar da haka ranar Laraba.

Ya ce motar kudin ta dauko kudi daga Enugu za ta kai garin Abakaliki, su kuma ‘yan sandan sun dira musu a garin Ezzamgbo dake karamar hukumar Ohaukwu.

“Maharan sun kashe ‘yan sanda hudu daga cikin jami’an tsaron dake raka motar sannan biyu sun ji rauni.

Ya ce maharan sun harbe tayoyin motar ne domin motar ya wuntsila amma hakan bai samu musu ba direban motar ya rike motar har sai da ya kai ga shingen Sojoji.

Tuni dai har an kai wadanda suka ji rauni asibiti.

Share.

game da Author