Mahara sun kashe mutum 14 a kauyen Agbudu dake karamar hukumar Kogi-Koton-Karfe a jihar Kogi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ede Ayuba ya sanar da haka ranar Laraba a garin Lokoja yana mai cewa ya sami labarin harin da misalin karfe 2 na daren Talata.
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa maharan sun kashe Mutum 14 sannan wasu shida sun ji rauni.
Binciken ya kuma tabbatar da cewa mutum 13 cikin mutum 14 da aka kashe duk ‘yan gida daya ne.
Ayuba ya ce ga dukan alamu maharan sun far wa kauyen ne a dalilin zaman doya da manya dake tsakanin su da mutan kauyen.
Ya ce a yanzu haka rundunar na gudanar da bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru a kauyen.
Ayuba ya ce rundunar na samun taimako wajen ma’aikatan karamar hukumar Kogi-Koton-Karfe sannan da sarkin kauyen Abdulrazaq Isa-Koto.
Mutum daya din da ya tsira da ransa daga cikin gidan da maharan suka kashe mutum 13 na taimaka wa rundunar wajen gudanar da bincike.
Idan ba a manta ba a cikin a ranar laraba ne aka ruwaito yadda Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya tsallake rijiya da baya daga harin kwantar baunar Boko Haram a hanyar sa ta dawowa garin Maiduguri daga kananan hukumomin Monguno da Baga.
Gwamnan Zulum ya ziyarci kananan hukumomin Monguno da Baga wajen rabawa mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra kayan abinci.