Baban Sakataren ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin juhar Kaduna, Ibrahim Jere ya shaida cewa daga ranar Litini duka ma’aikatan gwamnatin jihar Kaduna zasu koma aiki.
Jere ya ce sai dai kuma gwamtin ta gindaya wasu sharuddan da ma’aikata za su bi domin kiyaye dokokin dakile yaduwar cutar Korona.
” Manyan Darektoci, Shugabannin ma’aikatun gwamnati, kwamishinoni, manyan sakatarorin ma’aikatu za su rika zuwa aiki daga litinin zuwa Juma’a wato a kullum kenan.
” Ma’aikatan jihar daga mataki na 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki a ranakun Litini, Laraba da ranar Juma’a, daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana.
” Ma’aikata kuma daga mataki 7 zuwa 13, za su rika zuwa aiki a ranakun Talata da Laraba kawai.
Sakatare Jere ya kara da cewa daga yanzu za a rike dagatar da baki daga shiga ma’aikatun gwamnati sai an tantance su kafn su shiga idan ya zama dole.
Za a saka ma’aikaci ya rika tantance ainihin ma’aikata da wadanda baki ne a ma’aikatar.
Sannan kuma za a rika duba yanayin jikin mutum a duk lokacin da ya zo aiki, kuma za a tabbatar ma’aikata da saka takunkumin fuska, da kuma yin nesa-nesa da juna, wato bada tazara a tsakanin juna.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar Korona a kasar nan.
Alkaluman ranar Juma’a, Kaduna ta samu karin mutum 12 cikin mutum 600 da suka kamu.