Yadda Gwamna Zulum ya tsallake rijiya da baya daga harin kwantar baunar Boko Haram

0

Gwamnan jihar Barno ya tsallake rijiya da baya daga harin kwantar baunar Boko Haram a hanyar sa ta dawowa garin Maiduguri daga kananan hukumomin Monguno da baga.

Gwamnan Zulum ya ziyarci kananan hukumomin Monguno da Baga wajen rabawa mazauna sansanonin ‘yan gudun hijra kayan abinci.

Mjiya masu karfi da suka tabbatarwa PREMIUM TIMES, aukuwar wannan al’amari sun shaida cewa sojoji da ‘yan sandan dake gadin gwamna Zulum ne suka yi artabu da ‘Yan Boko Haram din har gwamna Zulum ya tsallake wannan hari.

Baya ga gwamna Zulum, wasu ma’aikatan hukumar bada agaji na jihar, sun afka wairin wannan tarko na Boko Haram.

Shugaban hukumar ta tabbatarwa PREMIUM TIMES da haka sai dai bata bada wani karin bayani a kai ba.

Share.

game da Author