Yadda Boko Haram suka kashe fasto 8 da mabiya Darikar Cocin Eklesiyar ‘Yan’uwa 8,000 – Billi

0

Shugaban Cocin Mabiya Darikar Eklisiyar ‘Yan’uwa na Najeriya, Joel Billi, ya bayyana cewa Boko Haram sun kashe mabiya cocin sama da 8370, ciki har da fasto-fasto su 8.

Da ya ke gabatar da bayani a Taron Manema Labarai na Duniya, a Yola, Jihar Adamawa, Billi ya ce ya kira taron ne domin bibiyar irin mummunar barnar da ya ce Boko Haram sun yi wa ‘yan Darikar su a Arewa maso Gabas.

Ya ce Kiristocin Eklisiyar ‘Yan’uwa na Kasa (EYN) su na Boko Haram suka fi kassarawa a cikin dukkan darikun Kiristoci a Najeriya.

Dalla-Dallar Barnar Da Boko Haram Suka Yi Wa Darikar EYN:

1. Sun kashe mana mambobi sama da 8370 har da fasto-fasto 8.

2. Akwai Kiristocin Cocin EYN sama da mutum 25,000 da suka tsallaka gudun hijira a sansanonin gudun hijirar Kamaru.

3. Sama da Kiristocin Darikar EYN 700,000 sun yi zaman gudun hijira a sansanonin Najeriya, kuma mafi yawan su na can har yanzu.

4. Rikicin Boko Haram ya shafi mambobin Cocin EYN sama da milyan 1.5 a Arewa maso Gabas.

6. Har yanzu ba a daina kama su ana kashewa ba.

7. An kone coci-cocin Darikar Eklisiya 300 daga cikin coci 588 da suke da shi a Arewa maso Gabas.

8. An kone gidajen Kiristocin Eklisiya ba adadi, an lalata wasu, an kwashe musu dukiyoyi.

9. Daga cikin Manyan Coci-cocin Gunduma 60 na Kiristocin EYN, 7 ne kadai Boko Haram ba su kone ko lalata ba a Arewa Maso Gabas.

10. Daliban Chibok mata 276 da Boko Haram suka sace, 217 daga cikin su xuk mabiya Darikar Eklisiyar ‘Yan’uwa ne.

11. Har yanzu akwai kauyuka da dama da mazaunan su suka kasa komawa, su na zaman gudun hijira a sansanoni.

Abin Da Muke So Gwamnati Ta Yi Mana:

1. A kafa Bataliyar soja a bayan Tsaunin Gwoza, domin kare rayuka da dukiyoyin mazauna garuruwa da kauyukan bayan tsaunin.

2. A gaugauta ganin mazauna yankin bayan Tsaunin Gwoza sun koma da zama kauyuka da garuruwan su.

3. Gwamnati ta gyara mana dukkan gidajen mu da Boko Haram suka kone ko suka tarwatsa.

4. Gwamnati ta gyara mana dukkan makarantun mu da Boko Haram suka tarwatsa.

5. Gwamnati ta gyara mana dukkan coci-cocin mu da Boko Haram suka tarwatsa.

6. A yi mana wadannan gyare gyare daga cikin kudaden da aka ware wa Hukumar Bunkasawa Da Farfado da Yankin Arewa maso Gabas.

7. A gaggauta maido da masu gudun hijira sama da 47,000 da ke zaune a sansanonin kasar Kamaru, zama na kaskanci da wulakanci.

Yayin da Shugaban Cocin EYN ya jinjina a kan hobbasan da sojoji ke yi a yanzu domin kawar da Boko Haram, Billi ya koka dangane da yadda kungiyoyin mahara da ‘yan bindiga daban-daban ke ta bayyana a kasar nan, su na kisa, garkuwa, kwashe dukiya da kuma yi wa mata fyade.

Share.

game da Author