Majalisar Tarayya ta zartas da cewa ta fara binciken yadda aka jidi sama da dala bilyan 1.05 a asirce daga Asusun Ribar Gas na Tarayya (NLNG).
Gaggauta fara binciken ya biyo bayan wani kakkausan korafi da Hon. Ndudi Elumelu ya gabatar a Zauren Majalisa a ranar Talata.
Elumelu ya ce an jidi dala bilyan 1.05 daga Asusun Ribar Gas a asirce, kuma ba a san abinda aka yi da su ba.
“Baya ga ba a san abin da aka yi da kudin ba, an kwashi kudaden ba tare da sanar wa sauran bangarorin gwamnatocin jihohi da ba kananan hukumomi an cire kudaden, wadanda har da su cikin masu hakki da kudaden.
“Sannan kuma wani abin mamaki shi ne yadda aka cire kudaden ba tare da neman izni ko amincewa ko gabatar wa majalisa kasafin abin da za a yi ko aka yi da makudan kudaden ba.” Inji Elumelu, wanda ya ce ta haramtacciyar hanya aka cire kudaden.
“Babu wanda zai iya sanin abin da aka yi da kudaden, daga Shugaban Kamfanin NNPC sai Babban Jami’in Kula da Kudade na NNPC kadai.” Inji Elumelu.
Nan da nan Majalisa ta mika aikin binciken ga Kwamitin Binciken Yadda Gwamnati Ke Kashe Kudade, kuma aka bai wa kwamitin makonni hudu ya kammala binciken sa, sannan ya sanar wa Zauren Majalisa abin da ya bankado.
Majalisa ta kuma gayyaci Shugaban Hukumar NNPC da Babban Jami’in Kula da Kudade na NNPC su bayyana a gaban kwamiti domin yin bayani.
Shi dai Asusun NLNG, kudade ne masu tarin yawa na ribar gas da ake sayarwa.
Dokar Najeriya ta rattaba cewa za a rika raba kudaden tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihohi da kuma Kananan Hukumomi.