SUNAYE: Dakarun Kwamandan PDP, Wike da Baradan APC da za su gwabza a Zaben Edo

0

Jam’iyyar ta bayyana sunayen mambobin kwamitin yakin neman zaben gwamnan Jihar Edo, kwana daya baya ta nada Gwamna Wike ‘Kwamandan’ Cin Zaben Gwamnan Kogi.

Kwana daya bayan jam’iyyar APC ta nada Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje Shugaban Kwamitin Cin Zaben Gwamnan Jihar Edo, ita ma PDP na nada Gwamna Nyesom Wike Shugaban Kwamitin ta na Cin Zaben Edo din.

Gwamnan Adamawa Umar Pintiri ne zai kasance mayaimakin sa a yakin neman zaben nasarar Edo da za a gudanar a ranar 17 Ga Satumba.

Gwamna Godwin Obaseki da ya fice daga APC ya koma PDP ne ya tsaya takara a karkashin PDP, yayin da su kuma APC ta tsaida Osagie Ize-Iyamu.

Iyamu dai shi ne ya yi wa PDP takara a zaben gwamnan Edo na 2016, kuma Obaseki ya kayar da shi a karkashin APC.

Yanzu dukkan su biyu sun koma wa jam’iyyun da suka yi adawa a 2016.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda APC ta tsaida Ganduje Shugaban Kwamitin Cin Zaben Gwamnan Edo.

Ganduje, gogarman da kyamara ta nuno ya na jidar dalolin talakawa, shi APC ta nada Shugaban ‘Rundunar’ Cin Zaben Edo.

Jam’iyyar APC ta kafa abin da ta ko kira kakkarfan Kwamitin Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar Edo.

An nada Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje Shugaban Kwamitin mai dauke da jiga-jigan APC har mutum 49, domin su tabbatar PDP ba ta kayar da APC ba a zaben, wanda za à gudanar a ranar 19 Ga Satumba.

APC ta nada Ganduje, gwamnan da a cikin 2018 kyamara ta nuno shi ya na jidar milyoyin daloli ya na cusawa aljifai, ya yi kaurin suna wajen cin zabe, tun bayan kakudubar da aka kitintima a zaben ‘inconclusive’ da aka sake yi a unguwar Gama, cikin Karamar Hukumar Nasarawa a Kano, a zaben 2019.

Dama kuma bayan Gwamna Godwin Obaseki na Edo ya koma jam’iyyar PDP, ita kuma APC ta tsaida Ize-Eyamu takara, Ganduje ya fito baro-baro ya ce, “Kano ta shirya tsaf domin tabbatar da cewa APC ta lashe zaben Gwamnan Edo.

Za a fafata ne tsakanin APC, PDP da sauran wasu jam’iyyu 10.

Bayan kyamara ta nuno Ganduje na jidar milyoyin dalolin talakawa, ya yi nasarar dakile binciken sa da Majalisar Dokokin Kano ta bijiro da shi.

Daga cikin mambobi 49 da ke cikin kwamitin da Ganduje ke jajoranta, akwai:

Gwamnan Imo Hope Uzodinma, Inuwa Yahaya na Gombe, Yahaya Bello na Kogi, Sanata Aliyu Wamakko, Minista Godswill Akpabio, Timipre Syla Karamin Ministan Fetur da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal.

Sunayen Kwamandojin PDP A Yankin Edo

Gwamna Nyesom Wike, Babban Kwamanda.

Gwamna Umar Fintiri, Mataimakin Kwamanda.

Dukkan Gwamnonin PDP 17

Atiku Abubakar.

Sanata David Mark.

Sanata Bukola Saraki.

Hon. Yakubu Dogara.

Sanata Enyinnaya Abaribe.

Sanata Ike Ekweremadu.

Sanata Rabi’u Kwankwaso.

Peter Obi.

Share.

game da Author