Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana cewa sufurin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki daga hutun Korona, ranar 29 ga Yuli.
Minista Amaechi ya ce an kara kudin kujerar jirgi a dalilin canja fasalin zama domin bin dokar bada tazara a tsakanin mutane.
Karamin Kujera da ake biyan naira 1300 ya koma naira 3000, kujerar naira 2500 ya koma naira 6000.
Amaechi ya ce sai da akayi tattaunawa mai zurfi, har da shugaba Buhari kafin a cimma wannan matsaya.
Bayan haka an kawo sabbin tarago domin fasinjoji.
” Za a zo da taragon dake daukan mutum 24, 56, 68, da mai daukan 88.
” Mutum zai zabi wanda yake so kuma kowannen su kudi sa da ban ne. Sannan muna kokarin ganin jirgin yay sawu 14 a rana maimakon 8 da yake yi a da.” Inji shugaban Hukumar Jiragen Sama ta Kasa, Mr Okhiria.
Okhiria ya kara da cewa nan da watanni uku za a fara saida tikitin kujeran jirgin ta yanar Gizo.
Discussion about this post