Hedikwatar Tsaron Sojojin Najeriya ta bayyana rundunonin ‘Operation Lafiya Dole’ sun yi arangama da Boko Haram bangaren ISWAP har sau 17 a cikin watan Yuni.
A wadannan arangamar, sojoji sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 75 tare da ceto mutane 35 daga hannun su.
Kakakin Yada Labaran su John Enenche, ya ce an kuma samu nasarar ‘yan ta’addar sosai inda da dama daga cikin su suka yi saranda.
Enenche ya ce a wadannan arangama, an kwace bindigogi da albarusai da gurneti da makamin roket da dama a hannun Boko Haram din a Arewa maso Gabas.
“An kuma kama manyan harsasan kakkabo jirage har 250 da kananan harsasai na bindigogi har 1,018. Sai tutucin Boko Haram guda biyo da kuma da kuma motoci.”
Ya kara da cewa an samu ceto mutum 35 daga hannun Boko Haram a cikin watan Yuni din. Cikin su akwai mata 18, maza 16 sai karamin yaro guda daya.
Enenche ya yi wadanda aka ceto din duk an yi musu allurar rigakafin cututtuka.
Hedikwatar Tsaro ta jinjina wa ‘Operation Lafiya Dole’, tare da kara musu kwarin guiwar ci gaba da aikin kakkabe Boko Haram.
“Hedikwatar Sojoji na kara kira ga daukacin jama’a cewa su rika sanar da bayanan duk giftawar wani bakon-idon da ba a yarda da shi ba.
“An kama wasu rikakkun kwamandojin ISWAP da suka hada da Mohammed Babagana, Modu Jugudun da Alhaji Usman.
Discussion about this post