Rundunar Sojojin Najeriya na fama da gaganiyar kara martabar aikin soja, yayin da sojoji 356 suka rubuta takardar ritaya, bisa dalilin cewa aikin “ya fita daga ran su.”
Haka wata kwakkwarar majiyar cikin sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES, domin a cewar majiyar, ta san duk abin da ake ciki dangane a batun ajiye aikin da sosojin 356 za su yi a karshen wannan shekara.
Wannan dalili ya na nuna cewa da yawan sojojin guyawun su sun yi sanyin da har ta kai su ga bukatar ajiye aiki saboda ya fita daga ran su.
Sojojin Najeriya a yanzu haka da dama na fafata gumurzun yakin da ya ki ci, ya ki cinyewa sama da shekaru goma tsakanin su da Boko Haram a Arewa maso gabas da wasu yankuna da dama a kasar nan.
Baya ga soja 356 da suka rubuta ritaya saboda aikin ya fita ran su, akwai kuma wasu 24 da suka ajiye aiki, saboda karbar sarautun gargajiya.
Adadin masu yin ritayar kenan ya cika 380.
Cikin su akwai MWO (Master Warrant Officers) 2, sai kuwa Warrant Officers 28.
A cikin wannan wata na Yuli, Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Tukur Buratai, ya amince da ritayar da sojojin 380 za su yi.
Za a tantancewar tabbatar da ajiye aikin su a ranar 20 Ga Disamba, bayan sun ajiye duk wani abu mallakar rundunar sojan Najeriya da ke hannun su.
A ranar 3 Ga Janairu, 2021 kuma za a amince kowa ya kama gaban sa, ya yi bankwana da aikin soja.
Wasu Sun Zubar Da Makamai Sun Arce
Sojojin Najeriya da dama sun watsar da makamai sun tsere daga filin gumurzu da Boko Haram.
Yawan wadanda suka tsere ba su cikin lissafin adadin 380 da za su yi ritaya karshen wannan shekara.
Yawancin masu tserewa na kuka ne da matsalar shugabannin sojoji, wadanda jama’a da dama na korafin a canja su, amma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kunnen-uwar-shegu da masu wannan kiraye-kiraye.
Kwamandan Operation Lafiya Dole, Olusegun Adebiyi ya fito a wani bidiyo ya na korafin rashin wadatattun kayan yaki da Boko Haram.
Kwanaki kadan bayan nan, sai aka cire shi, aka maye gurbin sa.
Cikin makon da ya ke karewa kuma, Boko Haram sun yi wa sojoji kwanton-bauna, har suka kashe 37.
Sojojin Najeriya na gaganiyar fuskantar yake-yake a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da ‘yan bindiga, Arewa ta Tsakiya da Yankin Neja Delta. Har ma da Kudu maso Gabas.
Akwai kuma wasu sojoji 6 da Hukumar Soja ta bada shawarar a sallama saboda matsalar rashin lafiya.
PREMIUM TIMES ta tuntubj Kakakin Sojoji Sagir Musa, wanda ya musanta ritayar da dimbin sojoji za su yi da kuma ikirarin guyawun sojoji na yin sanyi daga sha’awar aikin.
PREMIUM TIMES ta tsaya kan bakan ta, a wannan labari na ritayar daruruwan sojoji, cewa gaskiya ne.
Ta yarda da bincike da kuma majiyoyin da ta samu labarin.