Hukumar Tsaro ta SSS ta daukaka karar hukuncin tarar naira milyan 10 da Kotun Tarayya ta yanka musu, bisa samun su da laifin tauye hakkin wani da ya sayi tsohon layin wayar MTN, mallakar Hanan Buhari, ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari.
Cikin watan Mayu Premium Times ta buga labarin yadda Babban Mai Shari’a na Kotun Tarayya, Nnamdi Dimgba ya umarci jami’an SSS su biya Anthony Okolie diyyar naira milyan 10, be saboda tsare shi na tsawon lokaci da suka yi ba da umarni daga kotu ba.
Kotun wadda ke da zama a Asaba, babban birnin jihar Delta, inda Okolie ya shigar da kara, ta ce abin da SSS suka aikata haramtacce ne, saboda babu shi a cikin tsarin kundin dokokin Najeriya.
Makonni kadan bayan yanke hukuncin, sai lauyan Okolie ya fara bibiyar SSS domin su biya naira milyan 10 din da kotu ta umarci su biya Okolie.
Sannan kuma lauyan Mai suna Tope Akinyode, ya yi barazanar sake maka SSS kotu, saboda sun raina kotu, ta hanyar yin biris da umarnin da kotun ta bayar cewa su biya naira milyan 10, tunda sun ki biya.
Ana cikin haka ne kuma sai SSS suka daukaka kara cewa ta na neman kotu ta dakatar da Okolie daga tirsasa hukumar cewa sai ta biya shi diyyar naira milyan 10 din.
PREMIUM TIMES ta tuntubj lauyan Okolie, ya kuma tabbatar da cewa tabbas SSS sun daukaka kara. Amma ya kara da cewa za su bi SSS har cikin kotu domin su kalubalanci karar da suka daukaka.
Kotu ta sa ranar 8 Ga Yuli domin jin ba’asin kowane bangare.