Kwamitin Binciken yadda Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya rika danne bilyoyin nairori, ya fara fallasa wasu zarge-zargen da ake yi masa.
Kwamitin wanda ke karkashin tsohon Cif Jojin Najeriya, Ayo Salami, ya zargi magu da karkatar da bilyoyin nairori wadanda kudaden ruwa ne da aka samu daga naira bilyan 550 da EFCC ta ajiye a banki.
An kama Magu bayan an yi zargin ya na karkatar da kudaden da Hukumar EFCC ta karbo daga wadanda suka saci kudin Najeriya.
Cikin 2017 Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kafa Kwamitin Binciken Kudaden Da Ake Karbowa, tun daga ranar 28 Ga Mayu, 2015 zuwa Nuwamba 2018.
Tashin farko kwamiti ya gano cewa EFCC ba ta lissafa ilahirin kudin ruwan da ya taru ba na daga makudan kudade, sama da naira bilyan 550 da ta ajiye a banki.
Haka kuma kwamiti ya gano cewa EFCC ta karbo kudaden kasahen waje, sama da kwatankwacin naira bilyan 46, 038, 881, 508.78.
“Amma abin mamaki Magu ya bada rahoton wai kudaden kwatankwacin naira bilyan 37, 533, 764, 195.66 ne kawai.
Kwamiti ya ce Magu ne ya soke naira bilyan 8, 505, 118, 314.21.
Akwai kuma batun zunzurutun kudaden da aka fara magana daga farko, wadanda kwamiti ya ce Magu ya yi kwangen bayyana gaskiyar adadin kudaden.
Magu ya ce ya tara naira bilyan 504, 151,184, 744 04. Shi kuwa kwamiti ya ce abin da ya kamata Magu ya bayyana wa duniya su ne naira bilyan 543, 511, 793, 863.47.
Wato a nan Magu ya zabtare naira bilyan 39, 357, 608, 129.43.
“Wadannan kudaden da ya zabtare, ba a ma hada da zunzurutun kudin ruwan da suka taru a banki ba, sakamakon kudaden da Magu ya kwato ya ajiye a banki.” Inji Kwamiti.
Zargin Harkalla Da Hadin Bakin Kamfanin Canjin Kudi:
Ita ma Hukumar Leken Asiri Da Bin Diddigin Salwantattun Kudade (NFIU), ta zargi Magu da laifin yin sata-ta-saci-sata da kuma yawan karbar cin hanci.
Ta kuma gano cewa Magu na hulda da wani Kamfanin Canjin Kudi da ke Kaduna.
NFIU ta gano cewa kamfanin canjin kudin (Bureau de Change), ya na da asusun ajiyar kudade har 158 a bankuna daban-daban. Kuma ya na da alaka ta kut-da-kut da Magu.
Akwai kuma wani babban lauya a kasar nan mai kusanci da Magu, da bincike ya nuna cewa Magu ya taba kamfatar naira milyan 28 ya ba shi kyauta.
Zuwa yanzu dai lauyan Magu Oluwatosin Ojaomo ya nemi beli, kuma za a ci gaba da binciken Magu a ranar Litinin.