Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya nada Aminu Dan-Agungu sabon Sarkin Dawaki Babba shekaru 17 bayan mahaifinsa marigayi Ado Bayero ya tsige shi daga sarautar Sarkin Dawaki Maituta.
Maiba gwamnan Kano Abdullahi Ganduje shawara kan harkokin masarautu, Tijjani Mailafiya ya bayyana haka ranar Litini a Kano.
Tijjani ya shaida cewa gwamnatin Kano ta karbi wasikar neman a sake nada Dan-Agundi sarautar Sarkin Dawaki, sai dai wannan karon ba Maituta ba, Sarkin Dawaki Babba.
A wasikar, Tijjani ya bayyana cewa masarautar Kano na so ta nada Dan-Agundi ne saboda a tottoshe barakar da aka samu a masarautar Kano ba tun yanzu ba.
Tijjani ya kara da cewa nada Dan-Agundi da babban wan sarkin Kano Lamido Ado Bayero sarautar Wambai, yayi matukar dacewa kuma nuni ne cewa lallai masarautar Kano ta dauki hanya mai kyau.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya da ta ruwaito wannan Labari ta ce Sarki Aminu ya nada Lamido Ado Bayero sarautar Wambai daga sarautar Ciroma da yake rike da shi a da.
A karshe, Tijjani ya ce gwamnatin Kano zata mara wa wannan kokari na sulhunta ya’ayan masarautar da Sarkin Kano Aminu ya ke yi yana mai cewa a dalilin haka har majalisar jihar za a garzaya da neman damar nadin domin nade-naden su samu gindin zama.