Sakataren gwamnatin jihar Osun da wasu mutum 10 sun kamu da Korona

0

Gwamnatin jihar Osun ta sanar cewa Sakataren gwamnati Wole Oyebamiji da wasu mutum 10 da ke aiki tare da shi sun kamu da cutar Korona.

Kwamishinan kiwon lafiya Rafiu Isamotu, ya sanar da haka ranar Laraba.

Isamotu ya ce makonni biyu da suka gabata ke nan jihar na samun karuwar wadanda suka kamu da kwayoyin cutar.

Ya ce hakan na da nasaba da rashin kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar da mutane suka banzatar.

Isamotu ya ce a dalilin haka gwamnati za ta dauki tsauraran matakai da za su taimaka wajen ganin mutane sun kiyaye dokokin gujewa kamuwa da cutar.

” Za mu karfafa aiyukkan da jami’an tsaro ke yi sannan za Kuma mu kafa kotu domin yanke wa duk wanda aka Kama da laifin karya dokar guje wa kamuwa da cutar a jihar.

Sakamakon gwajin cutar da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata ya nuna cewa mutum 74 ne ke dauke da cutar a jihar.

A takaice dai mutum 127 ne suka kamu, 48 na kwance a asibiti sannan biyar sun mutum.

Idan ba a manta ba a ranar 30 ga watan Yuni Gwamnan Jihar Ondo ya shiga sahun jerin gwamnonin Najeriya da suka kamu da cutar Coronavirus.

Baya ga gwamna Rotimi, akwai gwamnan Bauchi
Bala Mohammed na Bauchi, Nasiru El-Rufai na Kaduna da Seyi Makinde na Oyo ne gwamnonin da suma sun kamu da cutar. Haka kuma gwamna jihar Delta Ifeanyi Okowa da matar sa suma sun kamu.

Sannan kuma Gwamnan Ebonyi na can a killace, bayan an samu ‘yar sa dauke da cutar Coronavirus.

Share.

game da Author