RASHIN JITUWA: Ali ya roki kotu ta raba auren sa da matar sa Sakina

0

A ranar Juma’a ne Mukaila Ali ya shigar da Kara a kotun Mapo dake Ibadan inda ya ke rokon kotun da ta raba aurensa da matar sa Sekinat.

Ali ya roki kotu ta raba aurensa da matar sa Sakinat saboda ya gano da ita da saurayinta, wani malamin makarantar islamiyya na shirya yadda za su kashe shi.

Ya shaida cewa akwai wata rana saurayin matarsa Sakinat ya shigo gidansa da wasu almajirai dalibansa suka yi masa satar kudi da kayan sawa a gidan.

“Mun fara samun matsala ne bayan na gargade ta game da abinda take yi cewa babu kyau. Wannan Malamin ya zo har gidana wata rana ya yi barazanar kashe ni idan ban saki Sakina ba ya aure ta.

” Tun daga wannan rana idan na kwanta barci sai na rika mafarkin dodo na bina zai kashe ni. Bayan haka sai na nemi taimako wajen maimagani, daga nan ne na daina mafarke mafarke irin haka.

Sai dai kuma matar sa Sakinat ta musanta duk abinda Ali ya fadi. Ta ce ta auri Ali shekaru bakwai da suka gabata bayan ta rabu da tsohon mijinta.

” Akwai alkawari tsakani da Ali tun lokacin da muka yi aure cewa zai kula da ni da ‘ya’ya na uku, amma Ali ya canja tsarin bayan da muka yi aure.

Sakinat ta ce tun bayan auren su Ali baya saduwa da ita a matsayinta na matarsa yakan far mata ne kamar ita dabba ce. Koda Ina jinin al’ada, Ali yakan tilasta min sai mun yi jima’i.

Alkalin kotun Ademola Odunade ya raba auren sannan ya mika wa Sakinat damar kula da dan su daya da haifa. Daga nan kuma Ali zai rika bata kudin shayarwa naira 5000 duk wata.

Share.

game da Author