Watanni 27 suka rage kafin zuwan lokacin fara buga gasar cikin Kofin Duniya na Qatar 2022, amma har Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA), ta fito da jadawalin yadda gasar za ta kasance.
Bayanan da FIFA ta fitar a ranar Laraba, sun nuna cewa za a bude wasan farko a ranar 21 Ga Nuwamba, 2022, babban filin kwallo na Al Bayt, mai cin ‘yan kallo har 60,000, wanda aka lullube shi rufin sitadiyo din da rufin tenti mau dauke da kayan alatu.
Za a ci gaba da gumurzun neman cin kofi har zuwa ranar wasan karshe, Wanda shi kuma za a gwabza neman zakara a katafaren filin wasa na Lusail, mai daukar ‘yan kallo har 80,000.
Kuma a cikin wannan sitadiyan ne za a yi wasan kusa da na karshe.
Kamar yadda gidan talbijin na ESPN ya bayyana, a wannan gasa masu kallo za su samu tagomashin kallon wasanni har hudu a kowace rana, a wasannin share-fagen guruf-guruf.
Sannan kuma da ya ke babu tazara sosai tsakanin biranen da ake buga wasannin, masu sha’awar kallo ido-da-ido za su iya tashi daga Doha zuwa duk garin da suke so su kalli wani wasa daga cikin kungiyoyin kasashe 32.
Karfe 1: 00 na rana za a fara wasa a kowace rana sannan a buga wasa na hudu kuma na karshe a wannan rana da karfe 10 na dare.
Shugaai Shirya Gasar Cin Kofin Duniya a Katar, Nasser Al Khater, ya ce shirye-shirye sun kusa kallama, domin ko a ayyukan gine-gine da titina an kammala kashi 85 bisa 100.
Ya ce FIFA ya za saurara har sai an yi bikin raba guruf-guruf a cikin Maris ko Afrilu, sannan ta bayyana sunayen garuruwan da za a kai kowane guruf.