OSINBAJO: Yaki da rashawa zai kara zama abu mai wahala a Najeriya

0

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawa zai ci gaba da kasancewa abu mai wahalar gaske a kullum a Najeriya.

Osinbajo ya yi wannan bayani a wani taron shekara-shekara na 20 da Hukumar Yaki Da Rashawa ta ICPC ta shirya a ranar Talata a Abuja.

Kakakin Osinbajo, Laolu Akande ne ya raba wa manema labarai takardar bayanan da ya karanta mai magana a kan kalubalen da ke tattare da yaki da cin hanci da rashawa da kuma hanyoyin da za a bi a ci nasarar shirin.

Ya ce baya ga wahalhalun da ke tattare da yaki da rashawa, ya ce jama’a da dama za su gaji kuma ran su ya baci, su daina sadaukar da rayuka da lokacin su wajen yakk da rashawa.

“Tsawon shekaru da dama an sace dimbin dukiyar Najeriya, an karkatar da wata mai dimbin yawa, an kimshe wata a kasahen waje. Wannan kuwa ya na dankwafar da kasashen Afrika, ya hana su ci gaba.”

“Afrika ba za ta iya cimma kudirin muradin karnin da ta ke so ta cimmawa ba, matsawar aka kasa dakile rashawa da cin hanci da rashawa da kuma yadda ake karkatar da makudan kudade zuwa kasashen ketare.” Inji Osinbajo.

Ya kara da cewa ba za a yi nasara a kan yaki da cin rashawa va, tilas sai an rika kare mutuncin wanda ya fallasa masu satar kudade .

“Ya zama tilas mu rika kare kima da matuncin magulmatan da ke fallasa Wanda su ka saci kudin kasar nan. Kada mu rika bayyana su ko bayyana sunayen su ”
Ya ce ya zama wajibi mu rika takura wa masu cin hanci da rashawa, har su rasa hanyar da za su rika waruwar kudaden. Idan muka yi hakan kuwa, to mun nuna wa duniya cewa hanyar cin hanci ba hanyar tsira ba ce.” Inji Osinbajo.

Share.

game da Author